Bisa kididdigar da ma’aikatar cinikayyar kasar Sin ta fitar, daga watan Janairu zuwa Maris na shekarara 2025, an kafa sabbin kamfanoni masu hannun jarin ketare 12,603 a fadin kasar Sin, adadin da ya karu da kaso 4.3 cikin dari idan aka kwatanta da makamancin lokacin a bara. Kana ainihin jarin wajen da aka yi amfani da shi a watan Maris ya karu da kaso 13.2 cikin dari idan aka kwatanta da makamancin lokacin a bara.
Bisa kididdigar, ainihin jarin da yankin ASEAN ya zuba a kasar Sin ya karu da kashi 56.2 cikin dari, kana jarin da kasashen EU suka zuba a kasar Sin ya karu da kashi 11.7 cikin dari, kuma ainihin jarin da kasashen Switzerland, da Birtaniya, da Japan da Koriya ta Kudu suka zuba a kasar Sin ya karu da kashi 76.8, 60.5, 29.1, da 12.9 cikin dari bi da bi.
Bugu da kari, ma’aikatar cinikayya ta kasar Sin ta sanar da cewa, za ta fadada ba da izinin yin gyare-gyare ga yankunan gwajin cinikayya mara shinge kamar lardunan Guangdong, da Tianjin, da Fujian, tare da ba su ayyukan gwaji da suka shafi sabbin gyare-gyare. (Mai fassara: Mohammed Yahaya)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp