An kammala bikin baje kolin kayayyakin masarufi na kasa da kasa na kasar Sin karo na 5 a jiya Jumma’a. Wani abin lura game da bikin shi ne, a wannan yanayi na karuwar kariyar cinikayya a duniya, amma kasuwar baje kolin kayayyakin masarufin ta bana mai taken “Raba damammaki na bude kofa da samar da ingantacciyar rayuwa tare” ta fi samun daraja da daukaka.
A cikin kwanaki 6 kacal, bikin baje kolin kayayyakin masarufin na duniya na kasar Sin, ya jawo hankulan kamfanoni 1767, da kayayyakin da kamfanoni suka sarrafa 4,209 daga kasashe da yankuna 71 na duniya, wanda ya kafa wani sabon tarihi na yawan kasashe da suka halarta, inda hakan ya kara fito da kyawun kasuwar kasar Sin.
Kazalika, a yanzu haka, ana gudanar da bikin baje koli na Canton Fair karo na 137 cikin farin ciki, kuma za a gudanar da nune-nunen kasa da kasa irin su baje kolin tsarin samar da kayayyaki, da baje kolin harkokin cinikayya, da na kayayyakin da ake shigo da su daga waje da sauran al’amura kamar dai yadda aka tsara.
Kasar Sin tana kara bude kofa ga kasashen waje, don haka masu zuba jari na kasashen waje za su gane wa idonsu irin damammakin da aka samar. (Mai fassara: Abdulrazaq Yahuza Jere)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp