A ranar Lahadi, wani mummunan haɗari ya faru a madatsar ruwa ta Gubi da ke Jihar Bauchi, inda ma’aikatan hukumar samar da ruwa ta jihar guda huɗu suka rasa rayukansu yayin aikin tsaftace madatsar ruwan.
Sunayen mamatan sun haɗa da Ibrahim Musa, Shu’aibu Hamza, Jamilu Yunusa, da Abdulmalik Ibrahim Hamza, wanda ya haɗa da uba da ɗansa da kuma ma’aikatan wucin gadi biyu.
- Hatsarin Mota Ya Hallaka Mutum Ɗaya A Bauchi, Wasu Sun Jikkata
- Hatsarin Mota Ya Hallaka Mutum Ɗaya A Bauchi, Wasu Sun Jikkata
A cewar ma’aikatan hukumar, lamarin ya faru ne yayin da suke aikin tsaftace tafkin da ke samar da ruwa ga al’ummar Bauchi, lokacin da suka hango kifaye a cikin ruwa. Wani daga cikin ma’aikatan ya yi ƙoƙarin kama kifin amma ya nutse, sannan wani ya tsalle don taimaka masa, kuma shi ma ya nutse. Duk da ƙoƙarin sauran ma’aikatan na ceto, dukkaninsu sun rasa rayukansu. An yi musu jana’iza a yau Lahadi.
Kakakin ma’aikatar ruwa ta jihar Bauchi, Umar Jibrin, ya tabbatar da faruwar lamarin amma bai bayar da cikakken bayani ba, yana mai cewa za a yi ƙarin haske daga baya.
Duk da haka, an samu labarin cewa manyan jami’an hukumar sun halarci jana’izar ma’aikatan a ranar Lahadi, amma ba a samu amsa daga Kwamishinan ma’aikatar albarkatun ruwa da babban manajan hukumar ba lokacin da aka yi ƙoƙarin jin ta bakin su.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp