Mataimakin darektan huhumar kula da harkokin kabilun kasar Sin Zhao Yong, ya ce kasar Sin ta samu sabon sakamako a tarihi, yayin gudanar da aikin hada kan kabilu daban daban na kasar, kuma yanayin kare hakkin dan adam na ‘yan kananan kabilun Sin ya kai matsayin koli a tarihi.
Jami’in ya bayyana hakan ne a Larabar nan, yana mai cewa, idan an waiwayi tarihin JKS cikin tsawon shekaru 100, za a lura cewa, babban sakamakon da aka samu a aikin hada kan kabilun kasar, shi ne an samu wata hanyar daidaita matsalar kabilu mai tsarin musamman na kasar Sin, wato dukkannin kabilun kasar suna zaman jituwa bisa tushen daidai wa daida. (Mai fassarawa: Jamila daga CMG Hausa)