Rundunar ‘yansandan Jihar Adamawa, sun damƙe mutane 148, tare da samun bindigogi 11 ƙirar AK-47 da wasu bindigogi 20 ƙirar gida.
Rundunar ta kuma samu wasu harsasai 110, da wasu abubuwan fashewa (IEDs) guda biyu, da kuma motocin sata guda uku.
- Gwamnati Za Ta Kwace Gidajen Ma’aikatan Da Suka Yi Ritaya Ba Su Biya Bashin Gidaje Ba
- An Fara Binciken Ƙwaƙwaf Kan Yaddda NNPCL Ke Hada-hadar Kuɗaɗensa – Ministan Kuɗi
Kakakin rundunar ‘yansandan Jihar, Dankombo Morris, ya bayyana hakan a yayin taron manema labarai da aka gudanar a birnin Yola, babban birnin Jihar Adamawa.
Ya bayyana cewa wannan nasara ta samu ne ta hanyar inganta aikin bincike da tsaro da aka sake tsarawa domin shawo kan barazanar tsaro da kuma rage laifuka a cikin jihar.
Morris ya ce matakan sun haifar da kyakkyawan sakamako wanda ya kai ga damƙe mutane da ake zargi da sace-sace, sata, kisan kai da fyaɗe, da kuma ƙwato makamai da harsasai.
Ya ƙara da cewa IEDs guda biyu da aka gano an birne su ne yankunan ƙaramar hukumar Hong, kuma an fashe su.
Morris ya kuma ce ‘yansandan sun ceto wasu da aka sace guda shida tare da haɗin gwiwar sauran hukumomin tsaro.
Ya jinjina wa jami’an tsaron da suka taka rawar gani wajen wannan aiki, kuma ya tabbatarwa da jama’a cewa rundunar za ta ci gaba da ɗaukar matakai don tabbatar da tsaro a jihar.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp