Asusun ajiyar kudade na kasar Amurka ya fitar da takardar bayani dangane da yanayin tattalin arzikin da kasar take ciki a jiya Laraba, inda aka nuna cewa, ganin yadda ake kara samun rashin tabbas a fannin tattalin arziki, makomar sassa da dama a kasar ta kara tabarbarewa. Tuni dai a ranar Talata, asasun ba da lamuni na duniya wato IMF ya fitar da rahoton hangen nesa kan tattalin arzikin duniya, inda ya rage hasashen da aka yi wa karuwar tattalin arzikin Amurka ta shekara ta 2025, raguwar da ta kai kaso 0.9 bisa dari, idan aka kwatanta da hasashen da aka yi a watan Janairun bana, al’amarin da ya sa Amurka ta zama kasa da aka fi rage hasashen karuwar tattalin arzikinta daga cikin kasashe masu ci gaba.
Kwanan nan ne Amurkawa daga duk fadin kasar suka fito kan tituna domin nuna adawa ga manufar gwamnatin kasar ta kakaba karin harajin kwastam. Baya ga jihar California, a ranar Laraba, akwai sauran wasu jihohi 12 da suka daukaka kara kan gwamnatin tarayya, inda suka bukaci a dakatar da irin wannan manufa, wadda a cewarsu, take kawo rudani sosai ga tattalin arzikin Amurka. Lamarin ya kuma bayyana dalilin da ya sa yawan mutanen da suka goyi bayan shugaban Amurka ta fannin tattalin arziki ya yi matukar raguwa daga farkon sabon wa’adin mulkinsa zuwa yanzu. Kwararan shaidu sun nuna cewa, kara sanya harajin kwastam bai haifar da karuwar samun kudi ga kasar ba, akasin haka ma aka samu, inda lamarin ya janyo tafiyar hawainiya ga tattalin arziki da kara tsawwala farashin kaya, gami da raguwar hasashen tattalin arziki da aka yi.
Ya kamata Amurka ta fahimci matsalolin da take fuskanta, da koyon darussa daga ciki, don warware matsalar cinikayya ta hanyar gudanar da shawarwari cikin adalci tare da abokan cinikayyarta. Idan Amurka ta ci gaba da kawo barazana ko yaudarar sauran kasashe, za ta kara dandana kudarta, kuma ba za ta kara samun nasara ba ko kadan. (Murtala Zhang)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp