Babban sakataren kwamitin kolin jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin (JKS) Xi Jinping, ya bukaci a yi kokari tare da karfafa samar da kyakkyawan tsarin sarrafa fasahar kere-keren kirkirarriyar basira ta AI, ta yadda za a ci gajiyar abin cikin aminci a bisa adalci.
Xi ya bayyana hakan ne a lokacin da yake jagorantar taron nazari na rukunin ofishin siyasa na kwamitin kolin JKS a jiya Jumma’a.
Ya nanata cewa ana iya aiki da AI a matsayin wata kyakkyawar harka ta al’ummar duniya da za ta amfanar da dan’adam. Don haka, yana da muhimmanci a gudanar da hadin gwiwar kasa da kasa a ko ina dangane da fasahar AI, da taimaka wa kasashe masu tasowa wajen karfafa kere-kerensu na fasaha, da kuma ba da gudummawa ga cike gibin rarrabuwar kawuna a duniya game da batun AI. (Abdulrazaq Yahuza Jere)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp