Gwamnatin tarayya ta umarci hukumar shirya jarrabawar WAEC da NECO da su fara amfani da cikakken tsarin amfani da Komfuta (CBT) ga dukkan jarabawar su nan da shekarar 2026. Ministan Ilimi, Dr. Tunji Alausa, ne ya bayar da wannan umarnin a ranar Litinin yayin ziyara da kuma duba yadda ake gudanar da gwaje-gwaje na CBT a cibiyoyin Bwari da kuma duba É—akin gwajin jarrabawa JAMB a kwamfuta.
Alausa ya bayyana cewa, daga watan Mayu ko Yuni na 2026, duka ɓangarorin tambayoyin da aka saba na WAEC da NECO, na rubutu da na gwaje-gwaje, za su kasance a komfuta gaba ɗaya. Ya ƙara da cewa wannan matakin na daga cikin manufar gwamnatin na magance matsalar satar jarabawa.
- Gwamnatin Kano Ta Biyawa ÆŠalibai 119,903 Kudin Jarrabawar NECO Da NBAIS
- WAEC Ta Kwace Lasisin Makarantu 574 Sakamakon Satar Amsa
Ministan ya kuma sanar da cewa an kafa kwamitin bincike Æ™arÆ™ashin jagorancin Daraktan JAMB, Prof. Ishaq Oloyede, wanda zai duba tsarin jarabawar Nijeriya gaba É—aya, inda aka ce sakamakon binciken zai fito nan da Æ™arshen watan gobe. Alausa ya yaba da ingancin gudanar da jarabawar UTME ta 2025 da JAMB, wanda ya bayyana a matsayin “matsayi na duniya” kuma yana cika Æ™a’idojin Æ™asa da Æ™asa.
A cikin jawabinsa, Oloyede ya bayyana cewa UTME ta 2025 tana ɗaya daga cikin mafi kyawun jarabawar da aka taɓa gudanarwa, inda ya kuma bayyana cewa duk wani zargin rashin dacewar cibiyoyin jarabawa yana buƙatar hujja mai ƙarfi.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp