Wani matashi mai suna Arigun David mai shekara 21 da abokinsa Michael mai shekara 34 sun rasa rayukansu bayan wani rikici da ya auku tsakaninsu da wani makiyayi a unguwar Agwan Doka, Mararaba, a ƙaramar hukumar Karu a Jihar Nasarawa.
Kakakin rundunar ‘yansandan Jihar Nasarawa, SP Ramhan Nansel, ya tabbatar wa LEADERSHIP a ranar Litinin cewa makiyayin ya sare su da adda sannan ya tsere.
- Sin Ta Harba Sabon Tauraron Dan Adam Na Ayyukan Sadarwa
- Akwai Ƙarin Gishiri A Yawan Masu Sauyin Jam’iyya Zuwa APC – El-Rufai
A cewar Nansel, da misalin ƙarfe 1 na ranar Lahadi, ofishin ‘yansanda ya samu kiran gaggawa cewa shanun wani makiyayi sun kutsa tare da cinye amfanin gonar da Arigun David ya shuka.
David ya fusata da abin da ya gani, wanda hakan ya sa suka faea hayaniya da makiyayin.
A lokacin rikicin, makiyayin ya sare shi da adda, inda ya mutu a nan take.
Michael, wanda ke zaune a Phase 4, ya yi ƙoƙarin ceton abokinsa, amma shi ma makiyayin ya sare shi da adda.
An garzaya da Michael zuwa Asibitin Mararaba domin ceto rayuwarsa, amma likita ya tabbatar da mutuwarsa bayan isar su.
‘Yansanda sun bayyana cewa an adana gawar Michael a asibitin domin gudanar da bincike.
Kwamishinan ‘yansandan jihar, ya umurci a tura jami’an tsaro domin kare rayuka da dukiya a yankin, tare da umartar Mataimakin Kwamishinan Sashen Binciken Laifuka da ya fara bincike da kuma kamo wanda ake zargi domin gurfanar da shi a kotu.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp