Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya yi kira da a gyara dabaru ta yadda za su dace da sauye-sauyen yanayi tare da rike dabaru masu muhimmanci da tsara nagartaccen shirin raya tattalin arziki da zamantakewar al’umma tsakanin shekarar 2026 zuwa ta 2030.
Wannan na zuwa ne yayin da Sin ke matsa kaimi a kokarinta na cimma burikan dake cikin shirinta na raya kasa na shekaru biyar-biyar karo na 14, tsakanin shekarar 2021 zuwa ta 2025, yayin da aka shiga shekarar karshe ta wa’adin shirin da kuma kokarin tsara shirin na shekaru 5 masu zuwa.
- ‘Yansanda Sun Kama Masu Garkuwa da Mutane 12 Da Masu Sayar da Makamai 3 A Taraba Da Kaduna
- Wasu Kwamandojin ‘Yan Ta’adda Sun Miƙa Wuya A Katsina
Xi ya bayyana haka ne yayin wani taron karawa juna sani kan raya tattalin arziki da zamantakewa cikin shirin raya kasa karo na 15 da za a aiwatar tsakanin shekarar 2026 zuwa ta 2030.
A cewarsa, wajibi ne shirin ya mayar da hankali kan burin cimma zamanantarwa irin ta gurguzu da nufin gina babbar kasa da samun ci gaba wajen farfado da ita. Shirin raya kasa na shekaru biyar-biyar, wanda shi ne daftarin dake zaman jigon jagorantar ci gaba na matsakaici da dogon zango a bangaren tattalin arziki da zamantakewar kasar Sin, yana zayyana baki dayan burikan kasar da manyan ayyuka da manufofin da ake aiwatarwa a dukkan bangarori cikin shekaru 5. (Fa’iza Mustapha)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp