Aikin gina tashar jirgin ƙasa ta zamani a Kano, ɗaya daga cikin manyan ayyukan gwamnatin Bola Ahmed Tinubu, yana ci gaba da tafiya babu kama hannun yaro.
Kamfanin da ke gina tashar, wato CCECC na ƙasar Chana, ya bayyana a yau cewa a yanzu haka an kusa kammala tsawon ginin tashar.
- Boko Haram Sun Kashe Masu Kamun Kifi 18 A Borno
- Gwamnonin Arewa Maso Gabas Sun Fara Taronsu Karo Na 11 A Yobe
Kamfanin ya ce yana sa ran kammala aikin tsawon ginin a farkon wannan watan na Mayu.
Faɗin ginin, wanda ya haura sukwaya mita 13,000, ya ƙunshi babban ginin tashar da ababen da ke tattare da shi, kuma zai kasance tashar da ta fi kowace girma a layin dogon da ake kira Kaka Reluwe.
Kaka Reluwe na nufin hanyar dogo daga KAduna zuwa KAno.
Kamfanin CCECC ya ce idan an gama aikin, zai taimaka gaya wajen haɓaka harkokin sufuri kuma ya kawo matuƙar sauƙi ga miliyoyin matafiya a ɓangaren Kano na hanyar jirgin.
Shi dai wannan layin dogo na Kaka Reluwe, hanya ce mai tsawon kilomita 204. Ta tashi daga Kaduna, ta bi ta Zariya, zuwa Kano.
Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ne ya ƙaddamar da ita a ranar 15 ga Yuli, 2021, sannan gwamnatin Bola Ahmed Tinubu tana ci gaba da aikin babu ƙaƙƙautawa don tabbatar da ta kammala ta a kan lokaci.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp