Hukumar Tare Kudaden Haraji ta Kasa (FIRS) ta umarci bankuna a fadin kasar nan da su gaggauta ganowa da kulle kowace asusun amsa da tara kudin haraji da bai da sahalewar amsar haraji a karkashin manhajar ‘TaxPro Max’.
Shugaban FIRS, Zacch Adedeji shi ne ya bayar da umarnin a kokarinsa na tabbatar da gaskiya da adalci da toshe kofofin sulalewar kudaden haraji, kamar yadda kakakin shugaban FIRS, Dare Adekanmbi ya fitar ta cikin wata sanarwar manema labarai a ranar Litinin.
- Gobara Ta Ƙone Shaguna 3 Da Kayayyaki Masu Yawan Gaske A Ibadan
- Bukatar Inganta Rayuwar Daurarru A Gidajen Yarin Kasar Nan
A cewar sanarwar, daga yanzu dukkanin kudaden haraji dole ne su bi ta tsarin nan na dandalin tara haraji da aka samar.
Hukumar ta FIRS ta yi gargadin cewa duk bankunan da ke shiga cikin tsarin tattarawa, kudaden da ake aikawa da su, da kuma tsarin sasantawa dole ne su bi wannan umarnin ba tare da bata lokaci ba, su daina amfani da asusun da ba su izini, sannan su tabbatar da cewa ana sarrafa hada-hadar kudaden ne kawai ta tsarin da aka samar daga dandalin manhajar ‘TaxProMax’.
“Muna fatan samun cikakken hadin kan ku don tabbatar da samun sauyi cikin sauki zuwa wannan tsari, ta yadda za a ba da gudummawa ga tsarin tattara haraji mai inganci,” in ji hukumar.
An samar da tsarin na dandalin ‘TadPro Mad’ da nufin saukake ayyukan haraji masu muhimmanci kamar rajistan masu biyan haraji, yin rajistan dawo da kudaden, sarrafa biyan kudi, da bayar da shaidar biyan haraji.
Manhajar an samar ne don daidaita tsarin gudanar da haraji da goyan bayan tsare-tsaren kyautata tsarin haraji da tafiya da fasahar zamani da FIRS ke bi.
Hukumar ta kuma bukaci masu biyan haraji da masu ruwa da tsaki da ke neman karin haske da su tuntubi hukumar.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp