Lokacin da aka nada gwamnan Jihar Filato, Mista Simon Lalong a matsayin Darakta Janar na yakin neman zaben dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC, an samu hadin kan shugabannin jam’iyyar wajen mara wa dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar, Sanata Bola Tinubu baya.
A daidai lokacin da APC ta sau nasarar hada kan ‘ya’yan jam’iyyar, ita kuma PDP ta dukufa wajen ci gaba da lallashin gwamnan Jihar Ribas, Mista Nyesom Wike, wanda ke zama babban barazana ga jam’iyyar wajen hada kan ‘ya’yanta da aka bata wa rai.
A kokarin PDP na sulhunta ‘ya’yanta, ta kafa wani tawaga wanda gwamnan Jihar Adamawa, Ahmadu Fintiri ya jagoranta wajen zama da tawagar gwamnan Jihar Ribas.
Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da wasu ‘ya’yan jam’iyyar suke bukatar shugaban jam’iyyar na kasa, Sanata Iyorchia Ayu ya sauka daga kan mukaminsa duk da kokarin sulhunta ‘ya’yan jam’iyyar.
Nada Lalong a matsayin Darakta Janar na yakin neman zaben dan takarar shugaban kasa na APC, mambobi da shugabannin jam’iyya mai mulki sun kulle wata baraka da ke iya jawo musu cikas a zaben 2023.
An dai samu rashin jituwa da tayar da kura a APC saboda takarar Musulmi da Musulmi, wanda lokacin da aka nada Lalong a matsayin Daraktan Janar na yakin neman zabe dan takarar shugaban kasa na APC wasu suka yi kokarin hana shi amsa, inda ya ce ko Pope Francis ba zai hana shi amsa ba, daga baya ya bayar da hakuri lokacin da cocin katolika ta yi masa ca kan kwatanta siyasar Nijeriya da Fafaroma.
Sai dai ba a ga duriyar wasu jiga-jigan ‘yan takarar shugaban kasa kamar irin su mataimakin shugaban kasa, Yemi Osinbajo da tsohon ministan sufuri, Chibuike Amaechi da kuma shugaban majalisan dattawa, Dakta Ahmad Lawan a wajen kaddamar da tawagar yakin neman zaman shugaban kasa na APC.
Amma kuma daraktan yada labarai na yakin neman zaben Tinubu, Mista Bayo Onanuga ya musanta rahoton da ke nuna cewa tawagar yakin neman zaben na samun turnuku. Ya kara da cewa tawagar yakin neman zaben ta hada kowa da kowa.
Onanuga ya ce Lalong shi ne ya jagoranci yakin neman zaben Amaechi da wasu gwamnoni lokacin zaben fid da gwani na jam’iyyar. Ya tabbatar da cewa tawagar ta kunshi kowa da kowa. Ya kara da cewa dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC, Sanata Bola Tinubu ya sulhunta da dukkan ‘ya’yan jam’iyyar.
Onanuga ya ce, “Lalong mutumin Amaechi ne. Sannan tawagar yakin neman zabe na Osinbajo suna aiki kafada da kafada da tawagar yakin neman zaben Tinubu da Shettima. To wani kuma matsala tawagan ke fuskanta?, in ji shi.
A nasa bangaren, shugaban yakin neman zaben Osinbajo, Mista Badmus Olawale ya bayyana cewa hadin kai ne kadai zai tabbatar da samun nasarar jam’iyyar a zabe mai zuwa. Ya kara da cewa mataimakin shugaban kasa ya bukaci magoya bayansa a kan su yi biyayya ga jam’iyyar APC.
A hannu guda kuma na kokarin yin sulhu a tsakanin Wike da dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar, an kafa tagawa ta musamman wanda Fintiri ya jagoranta.
Tsohon ministan sadarwa, Farfesa Jerry Gana ya koka kan yadda rikicin cikin gida ke kokarin tarwasa babbar jam’iyyar adawa, inda ya nuna takaicinsa kan rashin sasanta tsohon shugaban kasa da kuma gwamnan Jihar Ribas.
A cikin mambobin kwamitin da ke bangaren Atiku akwai Fintiri da tsohon ministan harkokin ‘yansanda, Adamu Waziri da tsohon gwamnan Jihar Kuros Ribas, Sanata Liyel Imoke da tsohon dan takarar gwamna na PDP a Jihar Ondo, Mista Eyitayo Jegede (SAN) da sauran wasu mutum uku wadanda ba a ambaci sunayensu ba.
A bangaren tawagar da ke wakiltar Wike kuwa, akwai tsohon ministan shari’a, Mohammed Bello Adoke da tsohon ministan yada labarai, Gana da tsohon gwamnan Jihar Ondo, Mista Olusegun Mimiko da kuma tsohon gwamnan Jihar Gombe, Alhaji Ibrahim Dankwanbo da dai sauran su.
A makon da ya gabata, PDP ta soke taron kwamitin zantarwa na jam’iyyar domin samun damar an sulhunta dukkanin ‘ya’yan jam’iyyar da aka bata wa rai.