Kwamishinoni na a matsayin ‘yan majalisar zartaswa na mai girma gwamna, wanda yake shi ne mai cikakken iko a cikin kowace jiha a Nijeriya.
Duk da iko da yake dunkule bisa kujerar gwamna, ba zai zamo tamkar wani gizo-gizo ba, wajen tafiyar da daukacin fannonin gwamnati a jihar.
Daga haka ne tunanin nada wasu mutane da za su taimaki gwamnan, wajen wakiltarsa cikin tafiyar da aiyukan jiha zai fara tasowa. Misali, bangaren ilmi, bangaren lafiya, bangaren noma, aiyuka, muhalli da makamantansu.
Mutanen da mai girma gwamna zai nada don rike irin wadancan bangarori da aka lasafta a sama, sune ake kira da kwamishinoni. Kuma sune ‘yan majalisar zartaswa da gwamnan kowace jiha ke zama da su a duk Mako sau guda a cikin gidan gwamnati, don tattauna irin nau’i-nau’i na aiyukan da al’umar jiha ke son a aiwatar musu, koko irin aikace-aikacen da gwamnati ke da tunanin gabatar da su ga al’umar jiha.
Kitso Da Kwarkwata A Kano
Wani abin mamaki da tuntuntuni shi ne, duk cikin kwamishinoni 21 da ake da su cikin Jihar Kano, ‘yan tsirari ne daga cikinsu za a ji al’umar jihar na yabo.
Da daman jama’ar jihar Kano, ‘yan siyasa da waninsu, sun fi jin-dadin mu’amala ma da hatta kansiloli ko ciyamomi sama da was masu rike da kujerun kwamishinoni a jihar. Yau da gobe, kujerar ta kwamishina cikin jihar ta Kano, na neman zama kushewar duk wani dan siyasa da aka bai wa rikonta, saboda tarin dalilai mabanbanta.
Sai ya zamana cewa, darewa bisa kujerar ta kwamishina a yau cikin jihar, wani abu ne mai hadarin gaske, musamman ga mutanen da suka yi suna da tambarin rowa tun gabanin hayewa bisa kujerun.
Wasu korafe-korafen da jama’a ke yi game da wasu gungun kwamishinoni cikin, abin dubawa ne, sannan, wasu korafin kuwa za a iya danganta su da na son zuciya.
Babu shakka halaiyar wulakanta mutane ba zai yi kyawo ba ga duk wani kwamishina, duba da cewa duk wata alfarma da wannan kwamishina ya samu daga gwamna har ya nada shi, da mutane ba su zabi wannan gwamna ba, to fa ba shi da ikon rabauta da waccan kujerar ta kwamishina. Da daman mutane cikin Kano a yau, na kokawa da irin abubuwan da akasarin kwamishinonin jihar ke musu, a duk sa’adda suka je ganinsu a ofis.
Kwamishina a Kano, na iya jibge mutane tsawon awanni 5 ko a bakin ofis, ya fadi cewa su jira shi zai gan su, amma daga bisani, sai a ga wannan kwamishina ya fito makale da dan wani fayil a hammatarsa, yana mai cewa jama’a, gwamna ya bugo masa waya, ya ce ya je gidan gwamnati ya same shi yanzu-yanzu.
Sai dai, ba safai ne za a ga wannan kwamishina ya fito haka a sukwane ba, sai bayan ya gama ganawa da masu manyan motoci ko masu manyan riguna da sitati da suka zo.
Menene amfanin kwamishina muddin zai gaza yin irin aikin da aka bukaci ya gabatar wa al’umma? Sai dai da daman kwamishinonin na yin hasashen cewa ai gwamna ne ba shi sakar musu mara su wataya.
To idan haka ne, me zai hana mutum ya sauka daga kan kujerar, ya yi wa jama’a bayani a kafafen yada labarai? Da irin wadancan kwamishinoni na yin haka, dole ne a taka wa maigirma gwamna burki.
Amma sabanin haka ne ke faruwa daga kwamishinonin! Mutum nawa ne ke yin kamun-kafa tun daga Abuja ko daga Masarauta don a nada su mukamin kwamishina?
Mutum nawa ne ke yin kamun kafa da iyalan gwamna ko shugaban jam’iyya suna masu godon a nada su bisa kujerar ta kwamishina a Kano?
Mutum nawa ne za a ga an sauke su daga kujerar, sai su koma tamkar wasu zautattu?
Daga wasu dalilan da ke nuna irin gajiyawa da kuma karfin-hali na irin wadancan kwamishinoni shi ne, mu dubi irin wahalar ruwan sha da ake fama da shi a Kano, amma sai ga kwamishinan ruwa ya sauka daga bisa kujerarsa ya tsaya takarar kujerar gwamna cikin jam’iyyarsa, kuma ma wai jam’iyyar tasa ta ba shi takarar! Ke nan, za a iya cewa, kwamishinonin sun raina hankali da tunanin akasarin jama’ar Kano.
Eh manah, a lokacin da cikin birni da karkara ake kokawa da kamfar ruwan sha a jiha, sai kuma a daidai wannan lokacin ne kwamishinan ruwa na jiha, zai nemi takarar kujerar gwamna, don al’umar jiha su sahale masa zama gwamnan jiha.
Ta yaya mutum ya gaza yin wani katabus bisa kujerar kwamishina, kuma ya bude baki ya ce zai iya jagorantar jihar gabadaya a matsayin gwamna? Idan lokacin da yake bisa kujerar kwamishina ya zamana gwamna ne ya hana shi damar aiwatar da aiki, me ya hana shi yin murabus?
To shin, a yanzu me zai rika cewa lokacin kamfen, don jama’ar Kano su yarda da shi, su zabe shi?
Kusan kwamishinoni kalilan ne za a ji jama’a na yabo kaf cikin kwamishinoni Jihar Kano.
Ko da yake, wasu daga cikin kunshin kwamishinonin, sun sauka, tare da tsayawa takarar kujerun mulki, wanda hakan ne ya ja hankalin mai girma gwamna zuwa ga nada wasu kwamishinoni 9 yanzu haka a Kano, don maye gurbin wadancan da su ka yi murabus.
Ba Cinyar Ba Kafar Baya
Da yawan mutane cikin Kano a yau, na masu fatan cewa, ka da fa mai girma gwamna ya kuskura ya sake yin wani kitson da kwarkwata wajen cike gurbin na kwamishinoni.
Tambayar da mutanen Kanon ke yi shi ne, da wadanne ma’aunai ne mai girma gwamna ke amfani da su, wajen zabo mutanen da ake sa-ran yi musu mukamin kwamishina a sati mai zuwa? Da daman mutane na masu ra’ayin cewa, babu shakka wadancan sabbin kwamishinoni masu jiran-gado, ko dai su taimaki jam’iyyar ne zuwa ga kai ta gaci a zabe maizuwa na 2023, ko kuma su kasance masu taimakawa ne zuwa ga kai jam’iyyar ga kushewa! Dole ne cikin dayan biyun nan ne zai faru.
Duk da cewa akwai yiwuwar cikin jerin sabbin kwamishinonin, za a iya samun masu bakin tarihi, to amma ya yi wuri tun yanzu a fara kushe su, zai fi kyawo ne a jira zuwa nan da wani lokaci halin kowa cikinsu zai fito sannu a hankali, daga nan, sai jama’ar Kano su ci gaba da gabatar da tsokacinsu game da su.
Kwamishinonin Ba Sa Tallata Gwamnati
Wani abu da ake ganin ya shahara a tsakanin kwamishinonin baya-bayan nan na Kano shi ne an shaidi da damansu wajen rashin tallata gwamnati mai ci.
Sai suka rikike kawai zuwa ga ta yaya ne za su yi su tara abin duniya? Kwamishina Musa Iliyasu Kwankwaso da kwamishina Muhammad Garba da Kwamishina Murtala Sule Garo, na daga sawun-gaba cikin kwamishinonin da ‘yan jam’iyyar gwamnati ke yabo dare da rana. ‘Yan jam’iyyar na yi musu kallon wasu kalilan daga jerin kwamishinoni a Kano da suke saurararsu gami da taimaka musu. Su ne kuma kalilan daga jerin kwamishinonin da a kullum ba sa gajiyawa wajen tallata irin aiyuka da kuma manufofin gwamnatin jihar Kano karkashin jagorancin Dr. Abdullahi Umar Ganduje (OFR).
Jan-hankali Ga Maigirma Gwamna
Babu shakka yana da kyau mai girma gwamna ya fara tunanin kawar da duk wani kwamishinan da ya ji al’umar Jihar Kano na gabatar da wasu korafe-korafe masu ma’ana a kansa, sabanin haka, an tasamma yi wa jam’iyyar gwamnati salalon-tsiya wajen samun kuru’un akasarin al’umar jihar Kano a zabe maizuwa na Shekarar 2023.
A karshe, me zai hana mai girma gwamna ya bayar da wasu lambobin yabo ga zakakuran kwamishinonin da aka hakkake suna kokari bisa kujerar kwamishinancin da aka danka masa?muk