Kasancewa babban dan kwallo ba karamar nasara bace, amma kuma zama babban dan wasa ba tareda lashe wani kofi ba ya na matukar sosa zuciyar kowane dan wasa.
Dan wasan da yafi kowane dan wasa zura kwallo a kungiyar kwallon kafa ta Tottenham (280) da kuma tawagar kwallon kafa ta kasar Ingila (71), Harry Edward Kane, ya shafe tsawon shekaru 15 ya na fafatawa a mabanbantan kungiyoyi ba tareda ya taba lashe wani kofi na azo a gani ba.
- Fasahohin Kasar Sin Na Taimakawa Afirka Tabbatar Da Wadatar Abinci
- Ina Son Ci Gaba Da Zama Kyaftin Din Ingila Har Zuwa 2028 – Harry Kane
Kane ya zauna a manyan kungiyoyin kwallon kafa kamar Tottenham, Lorient (Aro), Leicester (Aro), Milwall (Aro) da kuma Bayern Munich, amma dukkan wadannan wurare da Kane ya yi wasa bai taba dora hannunshi akan wani kofi a matsayin wanda ya lashe ba, ya buga wasannin karshe sau 6, ciki har da na Gasar Zakarun Turai da na European Cup ba tareda ya samu nasara ba.
Kane mai shekaru 31 ya samu kyautukan wanda yafi zura kwallaye a gasar Firimiya har sau 3 da kuma na gasar Kofin Duniya, wasu na kallon Kane a matsayin marar sa’a a fagen tamaula, amma yanzu ya baiwa marada kunya bayan lashe gasar Bundesliga ta kasar Jamus tareda Bayern Munich.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp