ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Sunday, December 21, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Majalisar Kano Ta Amince Da Dokar Wutar Lantarki Da Za Ta Raba Wa Jihohi 3 Wuta

by Sulaiman
8 months ago
Wutar lantarki

Majalisar dokokin jihar Kano ta amince da kudurin dokar kafa hukumar samar da wutar lantarki ta jihar Kano ta shekarar 2025 ya zama doka.

Kudirin dai na neman samar da damammaki ga jihohin Kano, Katsina da Jigawa domin amfani da sauran hanyoyin samar da makamashi kamar na hasken rana da na iska da na ruwa domin amfanin al’ummarsu da kuma ci gaban jihohinsu.

ADVERTISEMENT
  • Artabu Tsakanin ‘Yan Bindiga Da ‘Yan Banga Ya Ci Rayuka Da Dama A Bauchi
  • Manzon Shugaban Kasar Sin Ya Halarci Bikin Rantsar Da Shugaba Nguema Na Gabon

Daukacin kwamatin majalisar ne ya amince da kudurin bayan karatu na uku da magatakardar majalisar, Bashir Diso ya karanta, yayin zaman majalisar na ranar Litinin wanda shugaban majalisar Rt. Hon. Ismail Falgore ya jagoranta.

LABARAI MASU NASABA

Akpabio, Ganduje, Ogundoyin Sun Halarci Naɗa Seyi Tinubu Sarauta

Dambarwar Naɗa Muƙamai Da Soke Su A Gwamnatin Tinubu

Da yake karin haske game da abubuwan da aka tsara da kuma yadda hukumar za ta kasance, shugaban masu rinjaye na majalisar, Hon. Lawan Husseini ya shaidawa manema labarai cewa, sanya hannu kan dokar za ta kara samar da damarmakin wutar lantarki a jihohin uku.

Husseini ya jaddada cewa, za ta kuma rage wahalhalu da kuma rage tsadar makamashi ga ‘yan jihohin, za ta kuma samar wa kananan masana’antu da manyan masana’antu isasshen makamashi don yin kasuwanci, tare da bai wa asibitoci da cibiyoyin kula da ruwa damar gudanar da ayyuka yadda ya kamata.

Dangane da tsarin shugabancin hukumar da ake son yi, Husseini ya ce, za a samar da shugaba, manajan darakta da mataimakin manajan darakta wanda kowace jiha za ta samar da wakilai uku.

Ya kara da cewa, shugaban hukumar zai yi aiki na tsawon shekaru hudu wanda za a rika jujjuyawa a tsakanin jihohin da ke cikin tsarin.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Akpabio, Ganduje, Ogundoyin Sun Halarci Naɗa Seyi Tinubu Sarauta
Manyan Labarai

Akpabio, Ganduje, Ogundoyin Sun Halarci Naɗa Seyi Tinubu Sarauta

December 21, 2025
Tinubu
Manyan Labarai

Dambarwar Naɗa Muƙamai Da Soke Su A Gwamnatin Tinubu

December 21, 2025
Bambance-bambancenmu Shine Ƙarfinmu — Uba Sani
Manyan Labarai

Bambance-bambancenmu Shine Ƙarfinmu — Uba Sani

December 21, 2025
Next Post
An Kammala Bikin Baje Kolin Canton Fair Karo Na 137 

An Kammala Bikin Baje Kolin Canton Fair Karo Na 137 

LABARAI MASU NASABA

Davido Zai Raƙashe A Bikin Buɗe Gasar AFCON 2025 A Morocco

Davido Zai Raƙashe A Bikin Buɗe Gasar AFCON 2025 A Morocco

December 21, 2025
Yankin Rijiyoyin Mai Na Teku Mafi Girma Na Kasar Sin Ya Ba Da Rahoton Yawan Mai Da Iskar Gas Da Ya Fitar A Shekara

Yankin Rijiyoyin Mai Na Teku Mafi Girma Na Kasar Sin Ya Ba Da Rahoton Yawan Mai Da Iskar Gas Da Ya Fitar A Shekara

December 21, 2025
An Bukaci Bunkasa Fannin Kiwo A Hadin Gwiwar Sin Da Afirka

An Bukaci Bunkasa Fannin Kiwo A Hadin Gwiwar Sin Da Afirka

December 21, 2025
Akpabio, Ganduje, Ogundoyin Sun Halarci Naɗa Seyi Tinubu Sarauta

Akpabio, Ganduje, Ogundoyin Sun Halarci Naɗa Seyi Tinubu Sarauta

December 21, 2025
Tashar Teku Ta Ciniki Mai ‘Yanci Ta Hainan Ta Bude Sabon Babin Hadin Gwiwar Sin Da Kasashen Afirka

Tashar Teku Ta Ciniki Mai ‘Yanci Ta Hainan Ta Bude Sabon Babin Hadin Gwiwar Sin Da Kasashen Afirka

December 21, 2025
Tinubu

Dambarwar Naɗa Muƙamai Da Soke Su A Gwamnatin Tinubu

December 21, 2025
Zaben Fidda Gwani A APC: Sanatocin Jigawa Sun Rasa Tikitin Komawa Majalisa

APC Za Ta Gudanar Da Babban Taronta Na Kasa A Watan Maris

December 21, 2025
Mun Shirya Tsaf Domin Lashe Gasar AFCON Ta Bana – Bassey

Mun Shirya Tsaf Domin Lashe Gasar AFCON Ta Bana – Bassey

December 21, 2025
Sarakuna Na Da Rawar Takawa Wajen Kare Muhalli A Nijeriya – Ministan Muhalli

Sarakuna Na Da Rawar Takawa Wajen Kare Muhalli A Nijeriya – Ministan Muhalli

December 21, 2025
Me Ya Sa Ake Fifita Ilimin Boko A Kan Na Addini?

Me Ya Sa Ake Fifita Ilimin Boko A Kan Na Addini?

December 21, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.