Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umar Radda, ya ce gwamnatinsa za ta ci gaba da tallafa wa manoma domin bunƙasa harkar noma a jihar.
Gwamnan ya bayyana haka ne a ranar Litinin yayin da ya ƙaddamar da rabon buhunan takin zamani har 20,000 ga manoma a garin Kusada, domin shirin noman damina.
- Aikin Hajjin 2025 Ya Fara A Hukumance Yayin Da Tawagar NAHCON Ta Musamman Ta Tashi Zuwa Makkah
- An Kammala Bikin Baje Kolin Canton Fair Karo Na 137Â
Ya ce gwamnatin za ta sayar da buhun taki a kan farashin Naira 20,000 domin ya zama mai sauƙin samu ga manoma, wanda zai taimaka musu su yi noma fiye da da.
“Ina da tabbacin manomanmu za su amfana da wannan tallafi kuma hakan zai Æ™ara musu kuÉ—in shiga,” in ji Gwamna Radda.
Gwamnan ya ƙara da cewa irin wannan tallafi da aka bayar a bara ya taimaka wajen samun amfanin gona mai yawa da kuma wadatar abinci a jihar.
Baya ga takin zamani, gwamnatin ta kuma raba injunan huÉ—a guda 4,000 da injunan ban ruwa masu amfani da hasken rana 4,000 ga manoma a faÉ—in jihar.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp