Yawan tafiye-tafiyen da Sinawa suka yi a tsawon lokacin hutun ranar ma’aikata ta duniya da aka yi kwanan nan, ya kai miliyan 314, wanda ya karu da kashi 6.4% bisa na makamancin lokacin a bara. Yawan kudin da aka kashe kuma, ya kai dala biliyan 24.96, wanda ya karu da kashi 8.0% bisa na makamancin lokacin a bara.
Daga taron tattaunawa kan ayyukan tattalin arzikin Sin da kwamitin kolin jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin ya gudanar bara, zuwa rahoton ayyukan gwamnati na bana, an yi matukar muhimmanta habaka bukatu na cikin gida. Kuzarin kasuwar sayayya da yawon bude ido a lokacin hutun ranar ma’aikata ta duniya ta wannan shekara ya nuna sauyawar salon bunkasar tattalin arziki zuwa dogaro da kasuwar sayayya ta cikin gida, inda aka gano boyayyen karfin babbar kasuwar kasar.
Ban da wannan kuma, yawan baki daga kasashen waje da suka yi yawon bude ido a nan kasar Sin ya karu matuka sakamakon manufar yada zango ba tare da biza ba da ma yadda aka kyautata manufofin mayar wa baki haraji bayan komawa. Alkaluman da aka bayar na nuna cewa, a tsawon lokacin hutun, yawan shigowa yawon bude ido daga kasashen waje ya karu da kashi 173% bisa makamancin lokacin a bara. Kalmomi mafi jan hankali na bincike a shafin yanar gizo dake da nasaba da kasar Sin, wato “China Travel” da “China Shopping”, sun bayyana yadda Sin take kokarin bude kofarta ga ketare.
Duk da yadda Amurka ke haifar wa tattalin arzikin duk fadin duniya da barazana da kalubale bisa matakin harajin kwastam da ta kara kakkaba wa sauran kasashen, da yanayi maras tabbas da Sin take fuskanta a waje, ingancin tattalin arzikin Sin yana shaida abun da shugaban kasar Sin Xi Jinping ya fada, wato tattalin arzikin Sin tamkar teku ne ba karamin tabki ba. A sa’i daya kuma, Sin tana nacewa ga matsayin bude kofarta ga ketare don cin moriya tare a maimakon cin nasara daga faduwar wani bangare, matakin da ya taimaka ga kiyaye zaman lafiya da kwanciyar hankalin duniya, tare da samar da damammaki masu kyau ga bunkasar tattalin arzikin duniya. (Mai zane da rubutu: MINA)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp