Tawagar wanzar da zaman lafiya mai kai dauki cikin hanzari ta farko ta kasar Sin da aka aike zuwa Abyei, ta yi nasarar kammala aikin kiyaye zaman lafiya na tsawon shekara guda.
A jiya Jumma’a 9 ga watan Mayu, tawagar dakarun da ta kunshi hafsoshi da sojoji 75 na rukunin farko ta iso birnin Beijing cikin kwanciyar hankali.
- Xi Jinping Ya Gana Da Shugabannin Kasashe Daban-Daban A Moscow
- Zulum Ya Haramta Sayar Da Fetur A Bama Don Yaƙi Da Ta’addanci
A watan Mayun bara ne aka tura tawagar wanzar da zaman lafiya ta farko ta kasar Sin zuwa yankin Abyei. A yayin aikin nasu, hafsoshi da sojoji na tawagar sun yi aiki tukuru wajen gudanar da ayyukan wanzar da zaman lafiya kan-jiki-kan-karfi, inda aka bai wa dukkan dakarun tawagar lambobin yabo na aikin wanzar da zaman lafiya.
A shekarar da ta gabata, tawagar wanzar da zaman lafiyar mai kai dauki cikin hanzari ta gudanar da ayyuka sama da 300 da suka kunshi aikin rakiya na dakaru masu dauke da makamai, da sintirin dakaru masu makamai, da aikin rakiya zuwa muhimman wurare, tare da dakaru sau sama da 6,300, da motoci sau fiye da 990, da gudanar da tafiye-tafiye na sama da kilomita 14,000.
A bisa tsarin da aka yi dai, sojojin rukuni na biyu na tawagar farko ta dakarun wanzar da zaman lafiya ta kasar Sin da aka aike Abyei za su tashi zuwa gida a tsakiyar watan Mayun nan bayan sun kammala daukacin zagayen aikinsu tare da mika ragamar gudanarwa ga wasu. (Mai fassara: Abdulrazaq Yahuza Jere)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp