Gabanin babban zaben 2027, hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) ta ce har yanzu ba ta sanar da ranar da za ta fara sabunta katin rajistar masu zabe ba, wanda suka hada da canja wurin da kuma maye gurbin katin zabe da aka rasa.
Shugaban INEC, Farfesa Mahmood Yakubu, ya bayyana hakan ne a ranar Lahadi a cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun babban sakataren yada labarai na hukumr, Mista Rotimi Oyekanmi.
- INEC Ta Karɓi Takardun Yi Wa Sanata Natasha Akpoti Kiranye
- Shugaban INEC Ya Yi Kira Da A Sake Fasalin Tsarin Zabe Gabanin 2027
Ya musanta cewa hukumar ta sanya ranar 27 ga Mayu, 2025 a matsayin ranar da za a gudanar da sabunta katunan zaben.
“INEC na son sanar da jama’a cewa har yanzu ba ta sanar da ranar da za a fara sabunta rajistar katin masu zabe ba, wanda ya hada da canja wuri da maye gurbin katunan zaben da suka bace ba.
“Don haka hukumar ta bukaci jama’a da su yi watsi da sanarwar bogi, wacce ba daga hukumar ta fito ba da ke zagayawa a fadin Nijariya, tana ikirarin cewa hukumar ta saka ranar 27 ga Mayu a matsayin ranar da za ta fara sabunta katunan zabe da sauran ayyukan da ke da alaka za su.
“Bisa ga al’adarta hukumar, INEC za ta sanar da ranar da za ta fara sabunta katunan masu zabe a lokacin da ya dace, wanda kuma za a raba cikakkun bayanai ta shafukan sada zumunta na hukuma,” in ji Oyekanmi.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp