Trent Alexander-Arnold ya yanke shawarar barin Liverpool a lokacin da kwantiraginsa zai kare a karshen kakar wasa ta bana, yana mai cewa “shawara ce mafi wahala” a rayuwarsa gabanin komawarsa Real Madrid, Alexander-Arnold zai kare kwantiraginsa a karshen watan Yuni kuma makomar dan wasan na Ingila ka iya kasancewa Real Madrid
“Bayan shekaru 20 a kulob din Liberpool, yanzu ne lokacin da zan tabbatar da cewa zan tafi a karshen kakar wasa,” in ji dan wasan mai shekaru 26 a kan shafinsa na X, wannan ita ce shawara mafi wahala da na taba yankewa a rayuwata, akwai yiwuwar Arnold ya koma Real Madrid yayin da ake ci gaba da tattaunawa tsakanin wakilan kungiyar da na Arnold.
- Bayan Shekaru 10 Madrid Da Barcelona Zasu Sake Yaɗuwa A Wasan Ƙarshe Na Copa Del Rey
- Liverpool Sun Zama Zakaran Gasar Premier Bayan Lallasa Tottenham
Zai bar kungiyar a matsayin zakaran gasar Firimiya bayan da kungiyar ta Reds ta samu nasarar lashe kofin na bana inda ta kamo Manchester United a matsayin kungiyar da tafi kowace lashe babbar gasar Lig ta kasar Ingila da kofi 20, “Wannan kulob din ya kasance rayuwata gaba daya na zauna a nan na tsawon shekaru 20, tun daga makaranta har zuwa yanzu, goyon baya da kauna da nake ji dangane da wannan kungiyar zai kasance tare da ni har abada”.
Aledander-Arnold yana daya daga cikin manyan ‘yan wasan Liverpool uku wadanda kwantiraginsu zai kare a karshen kakar wasa ta bana. Mohamed Salah wanda ya fi zura kwallo a raga da kyaftin Virgil ban Dijk sun rattaba hannu a kan sabuwar yarjejeniya a makonnin da suka gabata amma Alexander-Arnold ya zabi barin kungiyar.
Mai tsaron bayan ya buga babban wasansa na farko a shekara ta 2016 kuma ya buga wa Reds wasanni 352 zuwa yau, inda ya zura kwallaye 23 tare da daukar kofuna da dama da suka hada da gasar Zakarun Turai ta 2019 da gasar Firimiya guda biyu, rahotanni sun bayyana cewa Liverpool ta yi niyyar sanya Aledander-Arnold zama daya daga cikin ‘yan wasan baya da ke karbar albashi mafi tsoka a tarihin gasar Firimiya a kokarinsu na ci gaba da rike shi.
Amma sha’awar taka leda a Real tare da babban abokinsa kuma abokin wasansa na Ingila Jude Bellingham ya sa shi canza ra’ayi, yunkurin da Alexander-Arnold ya yi zuwa Real Madrid ya raba kan magoya bayan Liverpool, inda wasu ke ganin ya kamata ya zauna ya zama gwarzon kulob daya.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp