Ɗan wasan gaban Super Eagles da Nottingham Forest, Taiwo Awoniyi, na samun kulawar likitoci bayan an yi masa tiyata a ciki, sakamakon rauni da ya samu yayin wasansu da Leicester City.
Awoniyi, mai shekaru 27, ya bugu da turken raga a wasan da suka tashi 2-2 ranar Lahadi.
- Tattalin Arziƙin Nijeriya Ya Bunƙasa, Amma Farashin Kayayyaki Na Ci Gaba Da Tashi – Bankin Duniya
- Amurka Da Saudiyya Sun Ƙulla Yarjejeniyar Dala Biliyan 600 Kan Tsaro, Makamashi Da Fasaha
Bayan jin raunin, an fitar da shi daga fili, sai dai daga baya ya dawo ya ci gaba da wasa, kafin a ƙara fitar da shi bayan ciwon ya tsananta.
Ƙungiyar Nottingham Forest ta tabbatar da cewa an garzaya da ɗan wasan zuwa asibiti a ranar Litinin, inda aka yi masa tiyatar gaggawa.
Rahotanni daga jaridar Mail Sport sun bayyana cewa raunin yana da hatsari, har ma ana kallonsa a matsayin barazana ga rayuwarsa.
Sai dai rahotannin farko sun nuna cewa yi nasarar yi masa tiyata, kuma likitoci na sa ran ya samu sauƙi nan ɗan lokaci.
Ƙungiyar Forest ta ce suna fatan ya murmure nan ba da jimawa ba.
Awoniyi bai samu wanda zai maye gurbinsa ba a wasan saboda tuni Forest ta gama canje-canjen da ta tanada, inda ta maye gurbin Elliot Anderson da Jota Silva kafin raunin ya faru.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp