Marigayi Alhaji Shehu Usman Aliyu Shagari shi ne zababben shugaban kasa daya tilo a jamhuriya ta biyu a tsakanin 1979 zuwa 31 ga Disamba, 1983, lokacin da Janar Muhammadu Buhari ya jagoranci yi masa juyin mulki.
A lokacin mulkin Shagari, an mayar da birnin tarayyar Nijeriya zuwa Abuja inda aka yi masa juyin mulki. A wannan lokaci, fadar shugaban kasar Nijeriya ba a Aso Rock take ba kamar yadda take a yau, wacce shugaba Bola Tinubu ke ciki a yanzu. Ofishin tsohon shugaban kasa Shagari, yana nan ne a Garki Area 1 a Abuja, wadda a yanzu ake kira da tsohuwar Sakatariyar Tarayya.
- Shawarwarin Raya Tattalin Arziki Da Cinikayya Tsakanin Sin Da Amurka Sun Haifar Da Managarcin Sakamako
- ‘Yan Bindiga Sun Sace Sarki Mai Daraja Ta Ɗaya A Kogi
Karamin ofishin Shagari, duk da cewa ya yi daidai da bukatun zamaninsa na sama da shekaru 40 da suka gabata, amma har yanzu yana nan a cikin tsohon ginin sakatariyar gwamnatin tarayya wacce a yanzu ta zama hedikwatar hukumar wayar da kan jama’a ta kasa (NOA).
A ranar Alhamis din nan, wasu hadiman shugaban kasa kan harkokin yada labarai sun kai ziyara hedikwatar hukumar ta NOA inda suka yi amfani da damar wajen lekawa daya daga cikin kayayyakin tarihin Nijeriya a baya – ofishin marigayi shugaba Shagari.
Bayan kammala ziyarar, daya daga cikin hadiman shugaban kasa kan harkokin yada labarai, Temitope Ajayi, ya wallafa hotunan a shafinsa na Facebook domin bayyana abin da suka gani.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp