• English
  • Business News
Thursday, November 6, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Ma’aikatar Kasuwanci Ta Sin Ta Yi Karin Haske Kan Huldar Cinikayya Tsakanin Sin Da Amurka

by CGTN Hausa and Sulaiman
6 months ago
Sin

Ma’aikatar kula da kasuwanci ta kasar Sin ta bayyana a jiya Laraba cewa, don tabbatar da matsaya daya da manyan jami’ai masu kula da cinikayya da tattalin arziki na kasashen Sin da Amurka suka cimma, bisa “dokar yaki da takunkumaman kasashen waje ta kasar Sin” da “doka kan jerin kamfanoni da daidaikun mutane da Sin ta haramta huldar cinikayya da su”, an dakatar da jerin matakan haramta cinikayya da Sin ta sanar da dauka kan wasu kamfanonin Amurka a ranar 4 ga watan Afrilu na tsawon wa’adin kwanaki 90, an kuma dakatar da matakan da ta dauka a ranar 9, inda dukkan dakatarwar suka fara aiki daga jiya Laraba, 14 ga watan nan da muke ciki.

A ranekun 4 da 9 ga watan Afrilun bana ne kasar Sin ta fara amfani da tsarin jerin kamfanoni ko daidaikun mutane da ba ta amince da su ba wato ta haramta huldar cinikayya da su, bisa dokar yaki da takunkumin da kasashen ketare ke kakkaba mata da tanade-tanaden wannan tsari da sauran abubuwan dake da nasaba da shi, inda ta shigar da kamfanoni 17 na Amurka cikin wannan jerin, tare da haramta musu gudanar da cinikin shige da fice da Sin ko zuba jari a kasar.

  • ‘Yan Bindiga Sun Sace Sarki Mai Daraja Ta Ɗaya A Kogi
  • ‘Yan Bindiga Sun Sace Sarki Mai Daraja Ta Ɗaya A Kogi

Ban da haka, kakakin ma’aikatar ya ce, bisa tanade-tanaden dake cikin tsarin jerin kamfanoni da daidaikun mutanen da Sin ba ta amince da su ba, kamfanonin Sin suna iya mika rokonsu na neman izinin yin ciniki da wadannan kamfanoni, bisa binciken da aka yi bisa wannan tsari.

Kakakin ya kara da cewa, bisa tanadin doka ko shari’ar dake da nasaba da kayyade fitar da kayayyaki zuwa ketare, ma’aikatarsa ta gabatar da sanarwoyi mai lamba 21 da mai 22 a ranekun 4 da 9 ga watan Afrilun bana, inda ta shigar da kamfanoni 28 cikin jerin kamfanonin da Sin ta kayyade fitar musu kayayyakin amfanin yau da kullum, wadanda za a iya yin amfani da su a bangaren aikin soja. Kuma daga jiya Laraba, cikin kwanaki 90 masu zuwa, za a dakatar da wadannan matakai, don tabbatar da matsaya daya da shugabannin kasashen Sin da Amurka suka cimma.

Dadin dadawa, kakakin ya ce, idan masu cinikin fitar da kayayyaki zuwa ketare a nan kasar Sin suna da bukatar fitarwa wadannan kamfanoni 28 dake cikin jerin sunayen kayayyakin da aka ambata, to za su iya gabatarwa ma’aikatar kasuwanci ta Sin rokonsu bisa doka da shari’a, kuma ma’aikatar za ta ba su izini bayan gudanar da bincike. (Amina Xu)

LABARAI MASU NASABA

An Yi Taron Kaddamar Da Tsarin Kawancen Kafafen Watsa Labarun Kasashe Masu Tasowa Da Dandalin Yada Labarai Na Bidiyo Karo Na 13 A Xi’an

CMG Ya Kaddamar Da Wasu Tashoshin Talabijin Uku A Dandalin FAST

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

An Yi Taron Kaddamar Da Tsarin Kawancen Kafafen Watsa Labarun Kasashe Masu Tasowa Da Dandalin Yada Labarai Na Bidiyo Karo Na 13 A Xi’an
Daga Birnin Sin

An Yi Taron Kaddamar Da Tsarin Kawancen Kafafen Watsa Labarun Kasashe Masu Tasowa Da Dandalin Yada Labarai Na Bidiyo Karo Na 13 A Xi’an

November 6, 2025
CMG Ya Kaddamar Da Wasu Tashoshin Talabijin Uku A Dandalin FAST
Daga Birnin Sin

CMG Ya Kaddamar Da Wasu Tashoshin Talabijin Uku A Dandalin FAST

November 6, 2025
Baje Kolin CIIE Ya Bayar Da Tabbaci Ga Duniya
Daga Birnin Sin

Baje Kolin CIIE Ya Bayar Da Tabbaci Ga Duniya

November 6, 2025
Next Post
Majalisa Ta Yi Watsi Da Ƙudirin Dokar Karɓa-karɓa A Kujerar Shugaban Ƙasa A Tsakanin Shiyyoyin Nijeriya

Majalisar Wakilai Za Ta Binciki Yadda Aka Samu Mummunan Sakamakon Jarabawar UTME 2025

LABARAI MASU NASABA

An Yi Taron Kaddamar Da Tsarin Kawancen Kafafen Watsa Labarun Kasashe Masu Tasowa Da Dandalin Yada Labarai Na Bidiyo Karo Na 13 A Xi’an

An Yi Taron Kaddamar Da Tsarin Kawancen Kafafen Watsa Labarun Kasashe Masu Tasowa Da Dandalin Yada Labarai Na Bidiyo Karo Na 13 A Xi’an

November 6, 2025
CMG Ya Kaddamar Da Wasu Tashoshin Talabijin Uku A Dandalin FAST

CMG Ya Kaddamar Da Wasu Tashoshin Talabijin Uku A Dandalin FAST

November 6, 2025
Baje Kolin CIIE Ya Bayar Da Tabbaci Ga Duniya

Baje Kolin CIIE Ya Bayar Da Tabbaci Ga Duniya

November 6, 2025
Gwamnatin Tarayya Ta Amince da Gina Sabbin Gidaje Ga Alƙalai, Da Samar Da Ruwa A  FCT

Gwamnatin Tarayya Ta Amince da Gina Sabbin Gidaje Ga Alƙalai, Da Samar Da Ruwa A  FCT

November 6, 2025
Manufofin Sin Na Yaki Da Sauyin Yanayi: Gani Ya Kori Ji

Manufofin Sin Na Yaki Da Sauyin Yanayi: Gani Ya Kori Ji

November 6, 2025
Shugaba Xi Ya Jaddada Bukatar Gina Ingantaccen Yankin Ciniki Cikin ’Yanci Na Tashar Ruwa Ta Hainan

Shugaba Xi Ya Jaddada Bukatar Gina Ingantaccen Yankin Ciniki Cikin ’Yanci Na Tashar Ruwa Ta Hainan

November 6, 2025
Amurka Ta Yi Barazanar Ƙwace Kadarorin Ƙungiyoyin Makiyaya A Nijeriya 

Amurka Ta Yi Barazanar Ƙwace Kadarorin Ƙungiyoyin Makiyaya A Nijeriya 

November 6, 2025
A Karon Farko An Gabatar Da Ka’idar Kasa Da Kasa Ta Fasahar 5G Mai Amfani Ga Masana’antu

A Karon Farko An Gabatar Da Ka’idar Kasa Da Kasa Ta Fasahar 5G Mai Amfani Ga Masana’antu

November 6, 2025
Gwamnatin tarayya

Ta’addanci Ba Zai Yi Nasara Ba A Ƙasarmu — Tinubu

November 6, 2025
Bikin Baje Kolin CIIE: Da Abokin Daka Ake Shan Gari

Bikin Baje Kolin CIIE: Da Abokin Daka Ake Shan Gari

November 6, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.