An kaddamar da sashin Blue Line na layin dogo a birnin Ikkon tarayyar Najeriya kwanan baya, inda karamin jakadan Sin dake Najeriya, Chu Maoming ya bayyana cewa, wannan wani muhimmin aiki ne da ke shaida hadin-gwiwar Sin da Najeriya a fannin raya ayyukan shirin “ziri daya da hanya daya”.
Chu ya ce, kasar Sin na da fasahohin zamani dake kan gaba a duniya a fannin shimfida layukan dogo, kuma a cikin shirin tsare-tsaren sufurin da kasar ta bullo da shi a bara, an shigar da aikin shimfida layin dogo tsakanin biranen Beijing da Taibei. Idan aikin ya kammala, ana maraba da kowa da kowa da su ziyarci yankin Taiwan na kasar Sin, don ganewa idanunsa kyan wajen tare da dandana abinci mai dadi.
Shi ma a nasa bangaren, gwamnan jihar Legas, Babajide Sanwo-Olu, ya ce, aikin ya kasance muhimmin kayayyakin more rayuwar al’umma da aka fi zubawa jari tun kafuwar jihar Legas, wanda zai yi matukar saukaka matsalar zirga-zirga a jihar, da zama wani abun misali ga ayyukan shimfida layukan dogo a Najeriya, da ma sauran kasashen yammacin Afirka. (Murtala Zhang)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp