Yawaitan soke zirga-zirgan jiragen sama da kuma yawan samun jinkirin tashi na ci gaba da zama ruwan dare a sassan kasar nan, inda gwamantin tarayya ta kaddamar da wani sabon tsarin inshorar jiragen hayar da za ta tabbatar da samun jiragen sama a duk fadin duniya, ta yadda za a samar da jiragen ga masu gudanar jirage a Nijeriya (AON).
Da yake jawabi a wajen bikin kaddamar da shirin, ministan sufurin jiragen sama, Festus Keyamo ya ce, “Mun damu matuka kan batutuwan da suka shafi jinkiri da soke tashin jirage, amma mun san cewa hakan na da nasaba da karfin ma’aikatan cikin gida, kowa na da irin iyaka karfinsa na samun damar shiga jiragen.
- Aikin Gina Tashar Jirgin Ƙasa A Kano Yana Ci Gaba Gadan-gadan
- ‘Yansanda Sun Musanta Zargin Kai Wa ‘Yan Bindiga Abinci Ta Jirgin Sama A Kogi
“Ku saurara, mun san ba abin farin ciki ba ne ma wani kamfani mai zaman kansa ya soke tashin jiragensa yana jinkirta tashinsa. Ba abin farin ciki ba ne a bangarensu, su kansu, ba farin ciki suke yi da hakan ba. Ina ba da hakuri, amma dole ne in fadi wannan kuma, in an samu irin wannan ba su ne ke da bacin rai ba, fasinjoji ke da bacin rai.
“Akwai matsala game da iya aiki. Suna da matsala, kuma akwai bukatar gwamnati ta duba wadannan matsalolin, ta yi kokari wajen magance wadannan matsalolin, sannan kuma za mu dora musu alhakin kansu.
“Babu wanda yake son ya kawo jirgi nan. Ba wanda ke son kawowa saboda tsare-tsaren inshora, saboda rashin amincewa da tsarin dokokinmu, rashin amincewa da hukumomin gwamnati daban-daban don tabbatar da amincin kayan aikinsu a nan.
“Amma sai ku ga cewa daya bayan daya, mun magance yawancin wadannan matsalolin. Har yanzu akwai sauran aiki a gabanmu, amma muna kan samun nasarori.”
Da yake jawabi a wajen taron, wakilin AON, Obiora Okonkwo ya yi maraba da wannan sabon ci gaban, inda ya bayyana cewa zai inganta ayyukansu.
A cewarsa, “Abin da muke gani a nan a yau wani babban ci gaba ne daga jerin abubuwa da dama.”
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp