Yana daya daga cikin abin da yake ba wa mutane mamaki ganin yadda a kowane sati kungiyar kwallon kafa ta Manchester United take shan kashi a gasar firimiya ta kasar Ingila amma kuma yake samun nasara a wasanninta na gasar Europa da take bugawa wanda har ya kaita ta samu nasarar kaiwa wasan karshe da za su fafata a ranar 21 ga wannan watan.
Ganin iriin halin da Manchester United ta shiga a gasar Premier League ta bana, za a iya munana mata zaton cewa ba za ta yi nasara ba a wasan karshe na gasar Europa League da za su fafata da kungiyar kwallon kafa ta Tottenham. Duk da cewa a baya sun taba lashe gasar amma wannan karon sai sun yi da gaske saboda Tottenham ba kanwar lasa bace.
- Har Yanzu Manyan ‘Yan Wasa Suna Son Buga Wasa A Manchester United – Amorim
- Za Mu Ci Gaba Da Binciko Mai A Arewa — Ojulari
Manchester United ita kadai ce kungiyar da ba ta yi rashin nasara ba cikin dukkan wadanda ke buga gasar zakarun Turai uku a bana, a Champions League, da Europa League, da kuma Conference League. Kazalika,
United din ce ta fi kowacce cin kwallaye a raga, inda ta zira 31 a kakar wasa ta bana a Europa, wanda hakan ba karamin ci gaba bane.
Tsohon danwasan Ingila da Manchester City Nedum kuma mai sharhin wasa a BBC, Nedum Onuoha, ya bayyana dalilan da suka sa Manchester United take sauyawa idan ta je gasar zakarun Turai ta Europa League a bana, inda ya ce ba ya ganin cewa Man United na sauya salo a wasannin zakarun Turai – kawai dai yanayin kungiyoyin da suke fuskanta ne.
A Premier League, kungiyoyi sun gama sanin Man United ciki da waje. “Dalili shi ne su kan hadu sau biyu duk shekara. Sun san abin da za su tarar game da ‘yanwasan United din da kuma filin wasanta, a gasar zakarun Turai kuma, akasari wannan ne karon farko da suke zuwa filin wasa na Old Trafford da kuma karawa da United. Ba su san yadda ya kamata su tunkare su ba” in ji shi.
Sai dai ya ce Manchester United dole sai ta yi da gaske a kan kungiyarTottenham saboda duka daga Ingila suka fito kuma sun hadu da su sau uku a wannan kakar duka Tottenham tana samun nasara kuma Tottenham din ta san lagon Manchester United sosai saboda haka komai zai iya faruwa a wasan da za su buga a wannan satin da za mu shiga.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp