• English
  • Business News
Saturday, June 7, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Hanyoyin Kare kai Ga Ɗalibai Da Ke Makarantun Kwana

by Rabi'at Sidi Bala
3 weeks ago
in Ilimi
0
Hanyoyin Kare kai Ga Ɗalibai Da Ke Makarantun Kwana
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsAppTelegram

Shafin TASKIRA shafi ne daya saba zakulo muku batutuwa daban-daban da suka shafi al’umma. Tsokacinmu na yau ya mayar da hankali ne kan daliban makarantun kwana, inda shafin ya ji ta bakin wasu daga cikin mabiya shafin TASKIRA game da wannan batu; “Ko ta wacce hanya ya kamata daliban makarantun kwana su kula da kansu wajen kiyaye matsalolin da ake samu game da wasu gurbatattun dalibai da malamai, domin samun inganraccen ilimin da aka je nema ba tare da matsaloli sun afku ba?

Ta wacce hanya iyaye ya kamata su kula ga ‘ya’yansu musamman wadanda suka kai yaransu makarantun kwana?, Fadi amfanin makarantun kwana da kuma rashin amfaninta, wacce shawara za a bawa dalibai masu sha’awar shiga makarantun kwana har ma da iyayen da suke sha’awar tura yaransu makarantun kwana?”.

  • Dalilai 12 Da Ke Nuna Malaman Makaranta Na Da Muhimmanci Ga Al’umma (2)
  • Dalilan Da Ke Nuna Malaman Makaranta Na Da Muhimmaci (5)

Ga dai bayanan nasu kamar haka;

Sunana Abba Abubakar Yakubu, dan jarida kuma marubuci da ke garin Jos, a Jihar Filato:

Dalibai

Labarai Masu Nasaba

Gwamnatin Kano Ta Ba Da Hutun Makaranta Domin Bukukuwan Sallah

Zulum Ya Ba Da Tallafin Karatu Ga Mata ‘Yan Asalin Jihar Da Suka Samu Maki 250 A JAMB

Makarantar kwana na da muhimmanci wajen samar da ilimi mai inganci, musamman domin dauke hankalin dalibai daga abubuwan da za su iya janye hankalinsu daga karatu. Akwai kulawa da sa’ido kan dalibi, don a san inda yake da abin da yake yi, lokaci zuwa lokaci. Wannan na daga cikin dalilan da ya sa iyaye da dama suka fi kai yaransu makarantar kwana, saboda tunanin za su fi samun kyakkyawan tsaro da kulawa. A wani bangaren kuma ana samun horo da tsauri ta yadda hakan ke ladabtar da yara masu rashin ji, su zama nutsattsu. Sai dai ana samun wasu abubuwan da suke tsorata iyaye daga cigaba da kai yaransu makarantun kwana, musamman a halin yanzu.

Daga ciki akwai matsalar tsaro da ke addabar wasu yankuna na Arewa, wanda ke jefa rayuwar yara a hadari. ‘Yan ta’adda na sace yara su yi garkuwa da su, don neman kudin fansa, a dalilin haka kuma har a samu batagarin da za su rika yi musu fyade. Akwai kuma matsalar lalacewar tarbiyya a cikin makaranta, idan dalibi ya gamu da abokai ko kawaye masu gurbatacciyar tarbiyya, suna koya masa halaye marasa kyau. Kamar irin su shaye-shaye, madigo, luwadi, bin maza, da sata. Mata da dama da yanzu suka shiga harkar madigo da zinace-zinace an ce daga makarantar kwana suke koyowa. Haka su ma maza da ke luwadi, yawanci sun koyo haka ne tun daga makarantar kwana, ta maza zalla ko ta mata zalla. A inda mata da maza ke hade a makaranta, musamman makarantun gaba da sakandire, nan kuma zinace-zinace ne aka fi samu da yawa. Lallai ya kamata iyaye su yi nazari sosai kafin su kai yaransu makarantun kwana, su tabbatar da ingancin makarantun, da ingancin tarbiyyar da suka yi wa yaransu, da ba da amanar su a hannun wadanda za su sa’ido a kansu. Amma kuma in sun ga akwai hadari a inda za a kai su to, gara a bar su a gida inda za su rika zuwa suna dawowa, ana ganin abin da suke yi.

Sunana Habibah Balarabe daga Abuja Nijeriya:

Hanyar da ya kamata dalibai su kare kansu daga afkuwar abin da ba a tsammani ita ce; da fari su san cewa karatu ne fa ya kawo su ba wani abu daban ba, su sani cewa a makaranta fa suke ba a gida ba dan akwai yaran da idan suka je wannan makarantar sun maida ita gidan kide-kide da raye-raye, don gani suke kamar wannan wajen nasu ne su-su kadai sun manta da cewar wannan wajen akwai wadanda suka tare (wato wadanda ba a ganinsu da idanu), haka ma yawace-yawace, da bin malaman makaranta domin samun maki. Iyaye su rinka ziyartarsu akai-akai ba tare da sun sani ba. Basu ingantacciyar tarbiyya tun suna yara, idan da hali su kai ‘ya’yan makarantar da sun san akwai mai kula da su.

Sunana Aminu Adamu Malam Maduri A Jihar Jigawa:

To magana ta gaskiya iyaye ya kamata tun farko su yi kokari tukuru wajen bawa ‘ya’yansu cikakkiyar tarbiyyar da zai yi wuya duk inda suka samu kansu su yi mu’amula da mara tarbiyya har su yi kokarin rudarsu, domin tarbiyya da iyaye za su bawa yara a farkon rayuwa tana da matukar muhimmanci dama tasiri a rayuwar su. To ya kamata dai iyaye su tabbatar da sun sauke nauyin tarbiyya ta farkon rayuwa kafin su kai ‘ya’yannsu makaranta, domin iyaye su za su sa dan ba na tarbiyya ba, su kuma Malamai su dora daga ginin iyaye don muddun iyaye suka yi abin da ya dace to komai zai tafi daidai.

To magana ta gaskiya amfanin makarantar kwana ya fi gaban kidayawa sai dai a kawo abun da ya samu, makarantar kwana tana matukar taimakawa wajen koyawa yara zamantakewar rayuwa da mutane daban-daban, koyon tsafta sosai da kuma uwa uba samun cikakken lokacin karatu ko kuma nace koyo. Wasu daga cikin matsalolinta samun bakin dabi’u da kuma karancin kulawa da gwamnati take yi a fannin ciyarwa. To shawara a nan ita ce ya kamata kowane dalibi yayi kokari ya zama wakilin gidansu nagari ta hanyar kyawawan dabi’u.

Sunana Lawan Isma’il (Lisary), Rano LGA Jihar Kano:

DalibaiAddu’a da kuma tuna cewa duk inda ka ke ko ki ke to amana ce ta iyaye a kanmu duk abin da muka yi Allah yana gani, mu dage da karatu da addu’a. Iyaye su ci gaba da yi musu addu’a sannan su rika kokarin ganin ko da biro ne aka ga alamar yara suna bukata to kafin ma yara su yi magana akan sa iyaye su yi kokarin siya musu, atakaice dai kada yara dalibai su zo da uzurin karatu iyaye su ki yi musu shi.

Amfaninta suna da yawa amma daya daga ciki ita ce; koyawa yara darasin rayuwa domin duk irin dadin da dalibi zai ji son samu yana gida wajen iyaye da ‘yan’uwa. Rashin amfaninta shi ma akwaisu da yawa amma daya daga ciki shi ne idan yara basu kai zuciya nesa ba to za su iya cin karo da miyagun malamai ko abokan karatu masu bata tarbiyya irin yadda wannan zamanin ya zo da shi, domin wasu daliban babu ce ko son cin edam yake sakasu fadawa cikin wata mummunar dabi’ar.

Shawarata a nan ita ce yara su shiga wannan makaranta da zuciya daya haka su ma iyayen suna saka yaransu da zuciya daya ba don gasa ba, sannan dukkanmu mu rika tuna cewa amanar junanmu ce a gare mu ako’ina muke kada mu shiga makarantun kwana muna kule-kulan abokan banza da malaman banza kuma uwa uba mu rika yawaita addu’a, Allah ya sa mu dace.

Sunana Princess Fatimah Mazadu daga Gomben Nijeriya:

Dalibai

Na farko dai kowanne dalibi ya kamata ya dubi tarbiyya da yardar da iyayensa suka bashi na turashi neman ilimi dan yayi alfahari da su da karatunsa watarana, ya kamata musamman ma diya mace wacce lalacewarta ba wahala, sosai ya kamata ta tsare mutuncinta da darajarta ta diya mace wajen yawan ibada, maida hankali wurin karatu, kawance/abota da kawayen kirki, da biyayya ga malamai wanda bai sabawa addini ba, yawancin lalacewar dalibai yana farawa ne daga malamai da abokai da masu kula da dakunan dalibai na makarantun kwana, suna amfani da nisanta iyaya ne daliban su lalatasu ‘more especially’ masu kwadayi da son kyele-kyele cikin daliban, sai yarinya ta kai zuciya nesa za ta tsare mutuncinta a makarantar kwana, duk da haka za ka ga yanayin tarbiyyarsu za ta canza akan wanda yake makarantar je-ka-ka-dawo koda ko ba mai muni bane. Yawan kai musu ziyara ta bazata, wadatasu da abinci, kula da sakamakon jarabawarsu duk sanda suka kawo, yawan buncikar lafiyarsu ko ta cikin dabara, janyo su a jiki dan sanin matsalolinsu da dai sauransu.

Akwai amfani kwarai, dan da yawa sukan samu wayewar zama cikin alumma, makarantar kwana, abu bai cika basu tsoro ba saboda horo na rashin naka a kusa. Shawara daya ce ilimi kan neman shi halak ne amma dai iyaye suna buncika wace makaranta za su rika kai yaransu da kuma sanya ido, ba wai in sun kai su sai su zauna su zuba ido kawai sai yaro ya zo hutu ba, dan ‘ya’ya nauyi ne akan iyaye dan ranar gobe kiyama Allah zai tambaye ka akan tarbiyyarsu Allah ya sa mu dace.

Sunana Anas Bin Malik Achilafia Yankwashi A Jihar Jigawa:

Wannan batu, batu ne mai matukar muhimmanci, domin shi dalibi a makarantar kwana yana bukatar kulawa daga bangaren malamai, da kuma shugabannin dalibai na makaranta, da kuma iyaye, ta fuskar mu’amalarsa da wasu mutanen, da kuma yanayin yadda yake tafiyar da rayuwarsa a kangin kansa.

Makarantar kwana tana da mahimmanci, domin dalibi zai koyi; Mu’amala da mutane, yadda ake ririta abin da yake a hannu, samun dabaru tafiyar da rayuwa, cudanya da mutanen da al’ada, da harshe ya bambanta, da sauransu. Ina bada shawara wa dalibi ya san irin abokan da zai yi mu’amala da su, ya kiyaye bijirewa dokokin makaranta, da shiririta na rashin maida hankali a kan karatu, muna fatan Allah ya sa mu dace, ya shirya mana zuri’a.

Sunana Aisha T. Bello daga Jihar Kaduna:

Gaskiya in iyaye sun kai yaransu makaranta ta kwana ya kamata su samu lokacin da za su je duba su akai-akai kuma su hada da rokon Allah shi ne kawai. Makarantar kwana tana da amfani ta wani bangare gaskiya sun fi koyawa da kyau sosai, in je-ka-ka-dawo ne yaro na da lokacin wasa amma ta kwana ba wanan lokacin karatu ne kawai. Shawarata a nan shi ne masu sha’awar shiga makarantar kwana ‘please’ in kin je ki kama kanki kuma ki yi kokarin ki yi abin da ya kawo ki saboda kada ki ba iyayenki kunya, Allah ya ba mu dacewa.

Sunana Muktari Sabo Jahun Jihar Jigawa:

Dalibai

Ana samun matsaloli akan dalibai a wasu daga makarantun kwana don haka ya kamata kowanne dalibi ya kula da kansa game da alakarsa da dalibi dan’uwansa da kuma malamai musamman wanda ke da alamun mummunar dabi’a. Ya kamata dalibi ya san dawa yake tarayyya daga malamai har dalibai don gudun haduwa da me mummunar dabi’a. Ya kamata iyaye su kula da biyan bukatun ‘ya’yansu lokacin da suke a makaranta kada matsalolin rayuwa su yi musu yawa. Makarantun kwana suna da amfani wajen killace yaro da bashi ilimi da tarbiyya ingantattu. Sannan yana daga rashin amfaninta idan yaro ya ki kula sai ya debo munanan dabi’u kamar shaye-shaye da sauransu. Shawara a nan ita ce dalibi ya san me ya kaishi makaranta ya kuma kula da shi sosai, ya kuma kaucewa munanan abokai. Iyaye kuma su san nauyin da ya hau kansu na kula da ‘ya’yansu da kuma sanin makarantun da za su kai yaransu.

Sunana Hafsat Yusuf daga karamar hukumar Isa a Jihar Sokoto:

Da farko, ya kamata dalibin kwana ya kula da wadanda zai yi abota da su ta bangaren karatu ko mu’amala. Abu na gaba shi ne, ya kamata iyayen yara su kula da ‘ya ‘yansu a lokacin da suke makarantar kwana ta hanyar kai musu wadataccen abinci da kuma yawan kai musu ziyara tare da bincika matsalolinsu dana karatunsu. Hakika makarantar kwana na da muhimmanci, ta hanyar koya ma dalibi iya mu’amala da mutane da kuma karantar rayuwa. Daga karshe, ina ba iyaye masu sha’awar inganta ilimin ‘ya’yansu shawara da su tura su makarantun kwana don samun abokan karatu da kuma samun wasu fa’idoji masu amfani ga rayuwa.

Sunana Hafsat Sa’eed daga Naija:

Makarantar kwana indai ba ta gaba da sakandare ba da babu yadda mutum zai yi babu a jihar sa to sai an nemi wajen kwana, amma ni a nawa ra’ayinma indai sakandare ne to, sam ban da ra’ayin na kai yaro ma. Shawarar da zan bawa iyaye wajen ganin tarbiyyar da suka bayar ba ta gurbata ba shi ne janyo yaro a jiki, duk da cewa zuciya-zuciya ne amma akwai wanda indai ka yi ka san tarbiyyar da ka bawa danka, kana ganin cewa ba ka da matsala a wannan bangaren to, sai ka saka shi. Amma dai yanada kyau ka ja danka a jiki ka rika bugar cikinsa kana jin matsalolinsa tare da bashi shawara koda kuwa abun karya ne dan ya kaucewa matsala sai ka fada masa. Dan wataran rashi da kwadayi shi yake sa yaron ya je ya gurbace amma idan ka tsarewa yaro dukkanin wannan abubuwan ka ja shi a jiki ina ganin cewa in sha Allah yaronka babu wata matsala da zai faru a irin haka. Amfanin makarantar kwana yaro zai nutsu yayi karatu ba kamar a gida ba.

Sunana Abdulrahman Aliyu ISA LGA Jihar Sokoto:

Mallam bahaushe ya ce kwadayi mabudin wahala, matsawar dalibi ya ce zai sa wa kansa kwadayi to tabbas yana cikin halaka, kuma kamar yadda aka sani a makaranta akwai lokuta daban-daban na gabatar da ayyukan makaranta, dalibi ya kamata ya kasance yana halartar duk wani aiki na makaranta da kauce wa biyewa abokanin banza, sannan kada dalibi ya saka kansa a abin da bai shafe sa ba. Abin da ya kamata iyaye su yi shi ne su; tabbatar da sun wadata yaransu da abinci da sutura da kayan tsabtace jikinsu, sa’annan su samu wani malami wanda zai lura dasu, duk bayan wata su kasance suna ziyartar makaranta don ganin yanayin da yaransu ke ciki.


Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

Tags: KwanaMakaranta
ShareTweetSendShare
Previous Post

Kyakkyawan Tunanin Kwankwaso Na Kafa Jami’ar Kimiyya Ta Wudil Ta Zama Alkairi Ga Al’umma – Alhaji Abdukadir

Next Post

Gidauniyar Mangal Ta Dauki Nauyin Yi Wa Mutum 12,300 Masu Cutar Kaba Aiki A Katsina

Related

Gwamnatin Kano Ta Ba Da Hutun Makaranta Domin Bukukuwan Sallah
Ilimi

Gwamnatin Kano Ta Ba Da Hutun Makaranta Domin Bukukuwan Sallah

5 days ago
Wasu ‘Yan Siyasa Da Jami’an Tsaro Na Taimaka Wa Boko Haram – Zulum
Ilimi

Zulum Ya Ba Da Tallafin Karatu Ga Mata ‘Yan Asalin Jihar Da Suka Samu Maki 250 A JAMB

6 days ago
Bayan Biyan Basussuka: WAEC Da NECO Sun Saki Samakon Jarrabawar Jihar Zamfara
Ilimi

Bayan Biyan Basussuka: WAEC Da NECO Sun Saki Samakon Jarrabawar Jihar Zamfara

6 days ago
Abin Da Ya Sa Ilimi Yake Da Muhimmanci Ga Rayuwar Al’umma (3)
Ilimi

Abin Da Ya Sa Ilimi Yake Da Muhimmanci Ga Rayuwar Al’umma (3)

6 days ago
Ɗalibai Sun Rubuta Jarrabawar WAEC Cikin Dare A Duhu
Ilimi

Ɗalibai Sun Rubuta Jarrabawar WAEC Cikin Dare A Duhu

1 week ago
Abin Da Ya Sa Ilimi Yake Da Muhimmanci Ga Rayuwar Al’umma (2)
Ilimi

Abin Da Ya Sa Ilimi Yake Da Muhimmanci Ga Rayuwar Al’umma (2)

2 weeks ago
Next Post
Gidauniyar Mangal Ta Dauki Nauyin Yi Wa Mutum 12,300 Masu Cutar Kaba Aiki A Katsina

Gidauniyar Mangal Ta Dauki Nauyin Yi Wa Mutum 12,300 Masu Cutar Kaba Aiki A Katsina

LABARAI MASU NASABA

Jami’i: Kasuwar Kasar Sin Ta Kasance Mai Jan Hankalin Zuba Jarin Waje A Ko Yaushe

Jami’i: Kasuwar Kasar Sin Ta Kasance Mai Jan Hankalin Zuba Jarin Waje A Ko Yaushe

June 6, 2025
Kasar Sin Ta Samu Ci Gaba Wajen Inganta Amfani Da Ruwa A Shekarar 2024

Kasar Sin Ta Samu Ci Gaba Wajen Inganta Amfani Da Ruwa A Shekarar 2024

June 6, 2025
Daurarru

Kashi 70 Na Fursunonin Nijeriya Ba A Yanke Musu Hukunci Ba

June 6, 2025
Alkaluman Adana Kaya Na Sin Sun Fadada Cikin Watanni 7 Da Suka Gabata

Alkaluman Adana Kaya Na Sin Sun Fadada Cikin Watanni 7 Da Suka Gabata

June 6, 2025
Wutar lantarki

Fadar Shugaban Kasa Na Yunkurin Biyan Basukan Wutar Lantarki Na Naira Tiriliyan 2

June 6, 2025
Jihohi Bakwai Na Kashe Kaso 190 Na Kudin Shigarsu Wajen Biyan Basuka

Jihohi Bakwai Na Kashe Kaso 190 Na Kudin Shigarsu Wajen Biyan Basuka

June 6, 2025
Gobara Ta Ƙone Wani Sashe Na Kasuwar Waya A Kano

Gobara Ta Ƙone Wani Sashe Na Kasuwar Waya A Kano

June 6, 2025
Ministan Harkokin Wajen Sin Zai Halarci Taron Ministocin Kula Da Matakan Taron FOCAC Da Bikin Baje Kolin Tattalin Arziki Da Cinikayyar Sin Da Afirka Karo Na 4

Ministan Harkokin Wajen Sin Zai Halarci Taron Ministocin Kula Da Matakan Taron FOCAC Da Bikin Baje Kolin Tattalin Arziki Da Cinikayyar Sin Da Afirka Karo Na 4

June 6, 2025
An Kama Wadanda Ake Zargi Da Kai Wa Shugaban Kwadago Hari Ribadu

Ribadu Ya Kara Jaddada Gargadinsa Kan Biyan Kudin Fansa Ga Masu Garkuwa Da Mutane

June 6, 2025
Kasar Sin Ta Harba Sabon Rukunin Taurarin Dan Adam Mai Samar Da Sadarwar Intanet

Kasar Sin Ta Harba Sabon Rukunin Taurarin Dan Adam Mai Samar Da Sadarwar Intanet

June 6, 2025
Talla

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In

Add New Playlist

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.