Majalisar dattawa ta bukaci gwamnatin tarayya da ta kafa sansanin soji a karamar hukumar Hong da ke jihar Adamawa domin dakile sake bullar ‘yan ta’addan Boko Haram a yankin Arewa maso Gabas.
Kudurin ya biyo bayan amincewa da kudirin da Sanata Aminu Abbas (PDP–Adamawa ta tsakiya) ya gabatar wanda ya samu goyon bayan daukacin Sanatoci daga shiyyar Arewa maso Gabas a zauren majalisar dattijai a ranar Laraba.
- Za A Gudanar Da Baje Kolin Tattalin Arziki Da Cinikayya Tsakanin Sin Da Kasashen Afirka Karo Na 4 A Birnin Changsha Dake Lardin Hunan
- ‘Yan Ta’adda Na Amfani Da Sojoji Da ‘Yan Siyasa Wajen Samun Bayanan Sirri – Zulum
Yayin da take yabawa kokarin jami’an tsaro, majalisar dattawan ta bukaci kafa sansanin soji na dindindin a Hong don karfafa jami’an sojin Nijeriya da sauran hukumomin tsaro a yankin.
Majalisar ta kuma umurci hukumar bayar da agajin gaggawa ta kasa (NEMA) da ta samar da kayayyakin agaji ga al’ummomin da hare-haren ya shafa domin bayar da agajin jin-kai.
Da yake gabatar da kudirin, Sanata Abbas, ya ce hare-haren da aka kai sun raba dubban mazauna karamar hukumar ta Hong da gidajensu, tare da lalata musu rayuwa.
Ya yi nuni da cewa, sake bullar ‘yan ta’addan ya zarce Adamawa hat zuwa jihohin Borno da Yobe, lamarin da ya kara ta’azzara matsalar rashin tsaro a yankin Arewa maso Gabas.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp