Kwanan baya, an fitar da wani fim mai taken “Gajimare a doron kasa” a sinimomin kasar Sin. Sashen samar da fina-finai masu bayyana al’amaru na gaske karkashin babban rukunin gidajen rediyo da talabijin na Sin wato CMG ne ya dauka tare da fitar da shi.
Fim din ya bayyana labarin iyalai guda biyu dake rayuwa a gundumar Awati ta kudancin jihar Xinjiang, wato iyalin Erkin da iyalin Zhao Qiang, wadanda suka rayu bisa sana’ar noman auduga.
- Sara Da Sassaka Ba Ya Hana Gamji Toho
- Jami’in Tsaro Ya Mayar da Dala 505 Da Riyal 30 Da Ya Tsinta A Yola
A yayin fama da aikin tsinkar auduga, sun gamu da matsaloli daban daban, amma a karshe iyalan biyu sun samu sakamako mai kyau bisa kokarin dukkan mambobin iyalan.
Yawan auduga da aka noma a jihar Xinjiang ta kai fiye da kashi 90 bisa dari na daukacin yawan audugar da dukkan sassan kasar Sin suka noma, kuma rayuwar miliyoyin manoman auduga na dukkan kabilun jihar Xinjiang na da alaka da auduga.
Gundumar Awati ta shahara wajen samar da auduga mai inganci, har ma ana kiranta da “Gidan auduga mai inganci a kasar Sin”. (Safiyah Ma)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp