Ofishin watsa labarai na majalisar gudanarwar kasar Sin ya gudanar da taron manema labarai a yau Laraba, inda jami’in ma’aikatar kasuwancin kasar da ke da ruwa da tsaki ya bayyana cewa, aiwatar da matakan da suka dace bisa “Ayyuka guda goma” na hadin gwiwa da Afirka, ya haifar da sakamako mai kyau, wanda ya zuba babban kuzari ga hadin gwiwar Sin da Afirka.
Mataimakin ministan kasuwanci na kasar Sin Tang Wenhong ya bayyana cewa, an riga an tattauna tare da kasashen Afirka sau da dama, an kuma amince da tsarin “Kasa daya, manufa daya” wajen tsarawa da aiwatar da matakai.
- Rashin Tsaro: Matasa Sun Yi Zanga-zangar Toshe Babbar Hanya Saboda Satar Mutane A Edo
- Za A Gudanar Da Baje Kolin Tattalin Arziki Da Cinikayya Tsakanin Sin Da Kasashen Afirka Karo Na 4 A Birnin Changsha Dake Lardin Hunan
A karkashin burin habaka kasuwanci, da hadin gwiwar tsarin masana’antu, an fara aiwatar da manufar soke harajin kwastam ga dukkan kayayyakin da ake shigowa da su daga kasashe masu karamin karfi, wadanda suka kulla huldar diplomasiyya da Sin, a ranar 1 ga Disamban shekarar 2024.
Karkashin ayyukan cudanya da juna, da samun ci gaba ba tare da gurbata muhalli ba, an kafa ayyukan hadin gwiwar samar da manyan ababen more rayuwa guda 18, wadanda suka shafi fannoni kamar layin dogo, da hanyoyi, da jiragen sama, da wutar lantarki, da kuma sadarwa. (Safiyah Ma)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp