ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Thursday, June 4, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Shirye-shiryen Tinubu Suna Buɗe Hanyar Farfaɗowar Tattalin Arzikin Nijeriya – Minista

by Sulaiman
1 year ago
Tattalin Arziki

Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, ya ce shirye-shiryen Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu a ƙarƙashin Ajandar Sabunta Fata suna ƙarfafa tushen farfaɗowar tattalin arzikin Nijeriya ta hanyar sauye-sauye masu ƙarfi, da zuba jari mai ma’ana da kuma manufofi da suka rungumi kowa da kowa.

A yayin da yake gabatar da jawabi a taron Makon Hulɗa Da Jama’a na Nijeriya (NPRW) na shekarar 2025 a Uyo, babban birnin Jihar Akwa Ibom, ministan ya ce hanyoyin da gwamnatin Tinubu ta ɗauka sun sake daidaita tafiyar Nijeriya zuwa babban gyaran tattalin arziki da ke nuna alamun nasara a fannoni da dama.

ADVERTISEMENT
  • Rashin Tsaro: Matasa Sun Yi Zanga-zangar Toshe Babbar Hanya Saboda Satar Mutane A Edo
  • Na Kwana A Marte Ne Don Ƙarfafa Gwiwar Jama’a Bayan Harin Boko Haram – Zulum

Ya ce: “Ku ba ni dama in bayyana tare da cikakken yaƙini cewa Ajandar Sabunta Fata tana shimfiɗa hanya mai ƙarfi zuwa farfaɗowar tattalin arzikin Nijeriya.”

LABARAI MASU NASABA

Gwamnatin Tarayya Ta Mayar Da Ofishin NAGGW Zuwa Kano Domin Yaƙi Da Hamada

Mambobin NYSC 4, Soja da Mutum 1 Sun Rasu A Hatsarin Mota A Adamawa

Ya ƙara da cewa, “Kuma wajibi ne a gare mu, a matsayin mu na ƙwararrun ma’aikatan hulɗa da jama’a, mu daidaita da wannan lokaci ta hanyar amfani da dabarun sadarwa masu ɗauke da ƙwarewa, ƙima, da haɗin kai, domin ƙarfafa gwiwar al’ummar mu, a gida da waje, su shiga cikin farfaɗo da tattalin arzikin wannan babbar ƙasa.”

Idris ya bayyana cewa aikin sake fasalin tattalin arziki ya faro ne tun daga ranar farko da Shugaban Ƙasa Tinubu ya hau mulki, lokacin da aka cire tallafin man fetur da kuma daidaita farashin musayar kuɗi — matakan da ya bayyana a matsayin “tushen farfaɗowar tattalin arzikin ƙasar nan.”

Ya haƙƙaƙe da cewa waɗannan matakai sun haifar da wahalhalu da farko, amma yanzu an fara ganin alfanun su, ciki kuwa har da daidaituwar musayar kuɗi, da ƙaruwar kuɗaɗen shiga ga jihohi, da farfaɗowar masana’antun tace mai, da kuma ƙarfafa matsayin kuɗin gwamnati.

Yayin da gwamnatin Tinubu take da da cika shekara biyu, ministan ya bayyana cewa ‘yan Nijeriya suna ganin gagarumin zuba jari da ake yi a harkar ababen more rayuwa, noma, tsaro, da bunƙasa rayuwar ɗan’adam.

A cewar sa, an ware naira tiriliyan 2.5 don ayyukan gina manyan hanyoyi a 2025 — adadin da ya fi na kowanne lokaci a tarihin Nijeriya.

Ya kuma bayyana ƙirƙirar sababbin ma’aikatu na bunƙasa yankuna da na kiwon dabbobi, domin ƙara bunƙasa arzikin ƙasa da noma da aka yi, da kuma ƙaddamar da shirin lamuni na NELFUND wanda ya taimaka wa ɗaliban Nijeriya sama da 300,000 da kuɗin karatu da gudanar da rayuwar su.

Daga cikin sauran muhimman ayyuka da ministan ya lissafa akwai shirin Shugaban Ƙasa na amfani da iskar gas ta CNG a motoci wanda ya jawo zuba jari kai-tsaye na fiye da dalar Amurka miliyan 450; da kafa CreditCorp domin bai wa ‘yan Nijeriya damar samun rance don gina gidajen su da kula da lafiyar su; da kuma ware naira biliyan 200 don tallafa wa ƙananan ‘yan kasuwa, ƙananan sana’o’i (SMEs) da manyan masana’antu.

Ya ƙara da cewa: “Yanzu haka Nijeriya ta zama wani gagarumin wurin gine-gine, inda aka kasafta sama da naira tiriliyan 2.5 don gudanar da ayyukan hanyoyi a wannan shekara kaɗai — wanda hakan bai taɓa faruwa ba a tarihin ƙasar nan.

“Gwamnati tana haɗa birane ta hanyar manyan ayyuka irin su hanyar Legas zuwa Kalaba da wata hanyar daga Badagry zuwa Sakkwato, da sauran sassa na ƙasa.

“Akwai sauran ayyuka da dama da ke gudana yanzu haka. Daga farfaɗowar matatun mai na Fatakwal da Warri, zuwa amincewa da a kashe naira biliyan 80 don sake gina dam ɗin Alau da ke Jihar Borno, zuwa ci gaban aikin gina layin dogo na zamani daga Kano zuwa Kaduna — babu wani yanki na ƙasar da aka bari a baya a cikin wannan babban zuba jari a ababen more rayuwa ƙarƙashin Shugaban Ƙasa Tinubu, wanda yanzu ake kira ‘The Road Master.’”

Ministan ya kuma nuna wasu alamomin da ke nuna bunƙasar tattalin arziki inda ya ce, “Ma’aunin Canjin Farashin Kayayyaki (CPI) na watan Afrilu 2025, wanda Hukumar Ƙididdiga ta Ƙasa ta fitar kwanan nan, ya nuna cewa hauhawar farashi ya tsaya a kashi 23.71, wanda an samu raguwar kashi 0.52 daga kashi 24.23 da aka samu a watan Maris. Wannan bai faru ba sai saboda tsare-tsaren Shugaban Ƙasa, waɗanda yanzu haka sun fara bayyana kuma suna haifar da ɗa mai ido.”

Idris ya buƙaci ƙwararrun masanan hulɗar jama’a da su taka rawar gani wajen gina da kuma nuna sabuwar martabar tattalin arzikin Nijeriya ga duniya.

“Nijeriya tana bunƙasa!” inji shi. “Nijeriya ta jawo fiye da dalar Amurka biliyan 50 na sababbin hannun jari kai-tsaye daga ƙasashen waje, kuɗin da ‘yan Nijeriya suke turowa daga ƙetare sun kai dala biliyan 21.9, kuma masana’antar finafinai (Nollywood) ta bayar da gudunmawar fiye da naira biliyan 730 ga haɓakar tattalin arziki (GDP).

“Waɗannan ba ƙididdiga ba ne kawai — su ne labarai da suke buƙatar a bada su ta hanya mai kyau, bisa ƙwarewa, kuma cikin ƙaunar ƙasa.”

Idris ya jaddada cewa ma’aikatar sa za ta ci gaba da inganta saƙonnin ƙasa ta hanyar sabon tsarin sadarwa na ƙasa mai suna National Strategic Communication Framework (NSCF).

Ya kuma taya Shugaban Hukumar NIPR, Dakta Ike Neliaku, murna bisa zaɓen sa a matsayin Wakilin Lardi na Musamman (Regional Delegate-at-Large) na ƙungiyar Global Alliance for PR and Communication Management.

Ya ce: “Ina taya ka murna, ya Shugaban mu, bisa wannan gagarumar nasara. A ƙarƙashin jagorancin ka, aikin hulɗar jama’a ya samu ƙarin daraja sosai a gida da wajen Nijeriya.”

Tattalin Arziki
Sulaiman
+ postsBio
  • Sulaiman
    Gwamnatin Tarayya Ta Mayar Da Ofishin NAGGW Zuwa Kano Domin Yaƙi Da Hamada
  • Sulaiman
    Mambobin NYSC 4, Soja da Mutum 1 Sun Rasu A Hatsarin Mota A Adamawa
  • Sulaiman
    Sarki Sanusi II Ya Tuɓe Rawanin Mai Unguwar Rikadawa Kan Badaƙalar Fili
  • Sulaiman
    Tawagar Masanan Dakile Yaduwar Cututtuka Ta Sin Ta Isa DR Congo

MASU ALAKA

Gwamnatin Tarayya Ta Mayar Da Ofishin NAGGW Zuwa Kano Domin Yaƙi Da Hamada
Labarai

Gwamnatin Tarayya Ta Mayar Da Ofishin NAGGW Zuwa Kano Domin Yaƙi Da Hamada

June 4, 2026
Mambobin NYSC 4, Soja da Mutum 1 Sun Rasu A Hatsarin Mota A Adamawa
Labarai

Mambobin NYSC 4, Soja da Mutum 1 Sun Rasu A Hatsarin Mota A Adamawa

June 4, 2026
Sarki Sanusi II Ya Tuɓe Rawanin Mai Unguwar Rikadawa Kan Badaƙalar Fili
Manyan Labarai

Sarki Sanusi II Ya Tuɓe Rawanin Mai Unguwar Rikadawa Kan Badaƙalar Fili

June 4, 2026
Next Post
Kotu Ta Soke Umarnin Kwace Filin Asibitin Tiamin, Ta Umarci Gwamnatin Kano Ta Biya Diyyar ₦2.6bn

June 3, 2026
Uba Sani Ya Sanya Hannu Kan Sabbin Dokoki A Bangaren Sauya Fannin Wuta, Noma, Da Muhalli

Uba Sani Ya Sanya Hannu Kan Sabbin Dokoki A Bangaren Sauya Fannin Wuta, Noma, Da Muhalli

June 3, 2026
Han Zheng Zai Halarci Taron SPIEF Karo Na 29 A Rasha Tare Da Gudanar Da Ziyarar Aiki A Belarus

Han Zheng Zai Halarci Taron SPIEF Karo Na 29 A Rasha Tare Da Gudanar Da Ziyarar Aiki A Belarus

June 3, 2026
Majalisa Ta Nemi Tinubu Ya Canza Dabarun Yaƙi Da Ta’addanci Don Kawo Ƙarshen Kashe-kashe

’Yan Majalisar Tarayya 3 Sun Fice Daga APC Zuwa ADC da PRP

June 3, 2026
An Fara Watsa Shirye-Shirye Masu Taken “Sha’awar Xi Jinping Ga Al’adu” Da Sauran Fina-Finan Bayyana Labaran Sin A Kasar Laos

An Fara Watsa Shirye-Shirye Masu Taken “Sha’awar Xi Jinping Ga Al’adu” Da Sauran Fina-Finan Bayyana Labaran Sin A Kasar Laos

June 3, 2026
Tambuwal Ya Jajanta Wa Waɗanda Harin ’Yan Bindiga Ya Shafa A Sokoto, Ya Nemi A Ƙara Tsaro

Tambuwal Ya Jajanta Wa Waɗanda Harin ’Yan Bindiga Ya Shafa A Sokoto, Ya Nemi A Ƙara Tsaro

June 3, 2026
Gwamnatin Beijing Ta Amince Da Kafa Cibiyar Kirkire-Kirkiren Fasahar Lissafi Mai Nasaba Da Sararin Samaniya

Gwamnatin Beijing Ta Amince Da Kafa Cibiyar Kirkire-Kirkiren Fasahar Lissafi Mai Nasaba Da Sararin Samaniya

June 3, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.