• English
  • Business News
Saturday, November 1, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Yadda Rikici Ya Yi Sanadin Kashe DPO A Kano

by Sulaiman
5 months ago
Kano

Rundunar ‘yansandan jihar Kano ta yi takaicin abinda da ya faru a ranar 25 ga watan Mayun 2025, da misalin karfe 08:15 na safe, a karamar hukumar Rano, inda sakamakon mutuwar wani bakanikin babur mai suna Abdullahi Musa, da aka kama shi tare da tsare shi bisa laifin tukin ganganci.

A wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na rundunar, SP Abdullahi Haruna Kiyawa ya fitar, ya kara da cewa, “Bayan tsare Bakaniken, daga bisani sai wasu alamun rashin lafiya suka bayyana a tare da shi, cikin gaggawa aka garzaya da shi Babban Asibitin Rano, inda ya rasu a nan, ranar 26 ga watan Mayun 2025, da misalin karfe 06:00 na safe, yayin da ake jinyarsa.

  • Amarya Ta Kashe Uwargida Bayan Ta Daɓa Mata Wuƙa A Katsina
  • Kofin Duniya: Kasar Saudiyya Za Ta Sassauta Dokar Hana Shan Giya A Wuraren Yawon Bude Ido 600

“Bayan faruwar lamarin ne wasu fusatattun matasa suka kai farmaki ofishin ‘yansanda na Rano, inda suka kona wasu motoci guda biyu, suka farfasa wasu motoci guda goma (10) tare da jikkata babban jami’in ‘yansandan (DPO), an garzaya da shi zuwa asibitin koyarwa na Aminu Kano, inda daga bisani ya rasu akan jinya. An kama mutane ashirin (27) da ake zargi da hannu a lamarin, amma an shawo kan lamarin, inda tuni aka mai do da zaman lafiya a yankin”.

LABARAI MASU NASABA

Tinubu Ya Kaddamar Da Ayyuka Bakwai A Jami’ar Ilori

Rikicin PDP Ya Ƙara Ta’azzara Yayin Da Ɓangarori Ke Dakatar Da Juna

Kwamishinan ‘yansandan jihar, CP Ibrahim Bakori, bayan ya ziyarci wurin da kuma kai ziyarar ta’aziyya ga Sarkin Rano, Mai Martaba Sarkin Rano, Ambasada Dr. Mohammed Isah Umar (Autan Bawo 19), ya ba da umarnin gudanar da cikakken bincike na gaskiya don gano musabbabin faruwar lamarin da gaggawa da kuma gurfanar da wadanda suka aikata duk wani laifi a gaban kotu.

Rundunar, ta jajantawa iyalan marigayin DPO da ya rasu yayin aiki, ta kuma yi kira ga mazauna garin da su kwantar da hankalinsu tare da kaucewa daukar doka a hannunsu. Sannan, su kuma bar binciken ya ci gaba da tafiya ba tare da katsewa ba.

Rundunar ‘yan sandan ta tabbatar wa al’umma aniyarta na ci gaba da wanzar da zaman lafiya a jihar tare da yin kira ga kowa da kowa da ya bai wa hukuma hadin kai a wannan bincike.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Tinubu Ya Kaddamar Da Ayyuka Bakwai A Jami’ar Ilori
Manyan Labarai

Tinubu Ya Kaddamar Da Ayyuka Bakwai A Jami’ar Ilori

November 1, 2025
Rikicin PDP Ya Ƙara Ta’azzara Yayin Da Ɓangarori Ke Dakatar Da Juna
Manyan Labarai

Rikicin PDP Ya Ƙara Ta’azzara Yayin Da Ɓangarori Ke Dakatar Da Juna

November 1, 2025
Dalibin Jami’ar Jos Ya Kashe Abokinsa Ya Binne Gawar A Rami
Manyan Labarai

Dalibin Jami’ar Jos Ya Kashe Abokinsa Ya Binne Gawar A Rami

November 1, 2025
Next Post
Ma’aikatar Kudi Ta Sin Ta Yi Tsokaci Game Da Matsayar Kamfanin Moody’s Bisa Kiyaye Mizanin Matsayin Kasar

Sin: Katsalandan Cikin Harkokin Kamfani Da Netherlands Ta Yi Ya Kawo Tsaiko Ga Tsarin Masana’antu Da Samar Da Kayayyaki Na Duniya

Sin: Katsalandan Cikin Harkokin Kamfani Da Netherlands Ta Yi Ya Kawo Tsaiko Ga Tsarin Masana’antu Da Samar Da Kayayyaki Na Duniya

November 1, 2025
An Gudanar Da Taron Tattaunawa Na Duniya Kan Kirkire-Kirkire Da Bude Kofa Da Ci Gaba Na Bai Daya A Nijeriya

An Gudanar Da Taron Tattaunawa Na Duniya Kan Kirkire-Kirkire Da Bude Kofa Da Ci Gaba Na Bai Daya A Nijeriya

November 1, 2025
Sabbin ‘Yan Saman Jannatin Kasar Sin Sun Shiga Tashar Sararin Samaniya Ta Kasar

Sabbin ‘Yan Saman Jannatin Kasar Sin Sun Shiga Tashar Sararin Samaniya Ta Kasar

November 1, 2025
Xi Jinping Ya Tattauna Da Shugaban Koriya Ta Kudu Lee Jae-myung 

Xi Jinping Ya Tattauna Da Shugaban Koriya Ta Kudu Lee Jae-myung 

November 1, 2025
Musabbabin Hana Sule Lamido Fom Ɗin Takarar Shugabancin PDP

Babban Burina Zama Fitacciyar Jaruma A Duniya —Aisha Umar

November 1, 2025
Xi: A Hada Kai Wajen Gina Al’ummar Bai Daya Ta Asiya-Pasifik

Xi: A Hada Kai Wajen Gina Al’ummar Bai Daya Ta Asiya-Pasifik

November 1, 2025
Dalibin Jami’ar Jos Ya Kashe Abokinsa Ya Binne Gawar A Rami

Dalibin Jami’ar Jos Ya Kashe Abokinsa Ya Binne Gawar A Rami

November 1, 2025
Sojoji Sun Kama Ƴan Ta’adda 20, Sun Ceto Mutane 17 Da Aka Yi Garkuwa Da Su

Sojoji Sun Kama Ƴan Ta’adda 20, Sun Ceto Mutane 17 Da Aka Yi Garkuwa Da Su

November 1, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.