Yara manyan gobe, haka ake cewa sakamakon yara su ne zasu gaji manya don ci gaba da wanzuwa a doron ƙasa, amma abin tambayar shi ne ko yaran Nijeriya suna murna da walwala?
Kafin ƙoƙarin amsa wannan tambaya ya kamata mu fahimci menene jin daɗi da walwalar yara.
- Yara Miliyan 2.9 A Nijeriya Ke Fama Da Rashin Abinci Mai Gina Jiki – UNICEF
- Firaministan Sin Ya Sauka A Indonesia Domin Ziyarar Aiki
Babban abin da yara ke buƙata shi ne tasowa tare da iyayensu biyu cikin zaman lafiya da kuma samu abinci mai gina jiki da kuma karatu mai inganci.
Yau bisa al’ada ake bikin ranar yara ta duniya wacce ake bayar da Hutun makaranta don yara su zauna a gida su huta tare da iyayensu.
Abu ne a fili cewa yaran Nijeriya suna cikin ƙunci da ƙalubale na rayuwa kamar yadda manya suke ciki. Babban abin takaicinma shi ne yadda ake ci gaba da samun rabuwa tsakanin iyaye wanda hakan ne sa yaran cikin taskar har girmansu.
Ga shi abin ci ya yi tsadar da samun a ci sau uku yana da wajala, balle kuma a nemi mai gina jiki. Kwananan masu sayar da ƙwai suka koka saboda rashin ciki, masu kifi dai haka abin yake balle kuma masu nama.
Duk da hakan bai hana yara murmushi ba wataƙila saboda ba su da masaniyar irin wahalar da iyayensu ke sha wajen ganin sun samar musu da rayuwa mai inganci.
Lallai ya kamata ƴan majalisa su matsala ƙaimi a samar da wani yanayi ga yara musamman wajen kare su daga faɗawa ƙangin talla ko bautar aikatau ko kuma zama ƴan jagorar masu bara, hakan kuwa zai faruwa ne idan aka aiwatar da dokar kare ƴancin yara.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp