An bude taron inganta karfin al’adun kasar Sin na 2025, jiya Litinin a Shenzhen na lardin Guangdong, lamarin dake nuna yadda Sin ke dagewa wajen karfafa al’adunta.
A matsayinta na wadda na kan kira da “mai jagorantar zamanintar da duniya”, kare al’adunta na gargajiya wani bangare ne na sirrin ci gaban kasar Sin har ma da zamanintar da kanta.
- Akwai Ma’ana Mai Zurfi A Bayan Da’a
- Gwamnatin Kano Zata Gina Masallacin Da Aka Ƙona Masallata A Gezawa
Idan ana batu na zamani da fasahohi, to kowa ya san Sin ce a kan gaba, sai dai duk da hakan, ko kadan ba ta yi watsi da al’adunta na gargajiya ba, asali ma, al’adun da akidun da suka samo asali daga kaka da kakanni, su ne ke jagorantar ayyukan raya kasa da ci gaban da Sin ke samu. A nan kasar Sin na fahimci cewa, wayewa ko ci gaba, ba shi ne yin watsi da al’adu ba, wayewa shi ne rike asalinka da kokarin raya shi da ma alfahari da shi.
Wannan taro da aka bude a jiya Litinin, ya hada masana da ’yan kasuwa da masu tsara manufofi, domin samar da wani dandali na musayar ra’ayi da basirar kara yayatawa da kare al’adun gargajiya na kasar Sin. Hakan ya nuna cewa, duk da wanzuwar al’adun a zukatan jama’a da yadda suke daukar su da muhimmanci, kasar Sin tana son kara karfinta a wannan bangare domin ci gaba ya raya shi ba tare da tsayawa ba.
Al’adu su ne ke nuna asalin kasa da al’ummarta, kuma shi ke hada kan al’ummar su zama tsintsiya madaurinki daya. A duniyar dake dunkulewa, abu ne mai muhimmanci a rike al’adu domin ci gaba da raya kasa da tabbatar da kasantuwarta. Kamar yadda na fada a baya, kare al’adun na daya daga cikin jigon ci gaban kasar Sin, inda ake iya ganin hakan cikin dukkanin manufofi da dabarunta na raya kasa.
Ya zama wajibi duk wata kasa dake son samun ci gaba mai dorewa, ta rike asalinta, ta kare al’adunta, ta zabar wa kanta hanya mafi dacewa da ita kamar yadda kasar Sin ta yi, domin har kullum, Sin za ta ci gaba da zama abin koyi ga sauran sassan duniya.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp