ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Sunday, November 16, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Sin Na Matukar Adawa Da Munanan Kalaman Sakataren Tsaron Amurka

by CGTN Hausa and Sulaiman
6 months ago
Sin

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin, ya bayyana matukar adawar kasarsa, da munanan kalaman da aka jiwo sakataren tsaron Amurka Pete Hegseth ya yi, a dandalin tattaunawa na Shangri-La karo na 22 da ya gabata.

Kakakin ya bayyana hakan ne a jiya Asabar, yana mai cewa da gangan mista Hegseth, ya kawar da kansa daga kiraye-kirayen wanzar da zaman lafiya da samar da ci gaba na kasar shiyyar, inda ya mayar da hankali ga furta kalaman yakin cacar baka don haifar da fito na fito, ya kuma bata sunan kasar Sin ta amfani da zargi marar tushe, da kiran kasar da wai “mai hadari”.

  • NDLEA Ta Cafke Masu Tura Alhazai Saudiyya Domin Safarar Hodar Iblis Zuwa Kasar
  • Bam Ya Kashe Mutane 9 A Wata Tashar Motoci Da Ke Borno 

Kakakin ya kara da cewa, ba wata kasa a duniya da ta cancanci a kira ta mai mulkin danniya sama da Amurka, wadda har kullum burinta shi ne gurgunta zaman lafiya, da daidaito a yankin Asiya da Fasifik. Don haka domin cimma burin babakere, da ingiza manufar tabbatar da tasiri a yankin tekun Indiya da Fasifik, Amurka ke ta jibge makamai a tekun kudancin Sin, tare da rura wutar tashin hankali, da haifar da yanayin matsi a yankin, wanda hakan ke juya alakar yankin zuwa wuri da tashin hankali ka iya barkewa, lamarin dake haifar da damuwa tsakanin al’ummunsa.

ADVERTISEMENT

Jami’in na kasar Sin, ya kuma jaddada cewa batun yankin Taiwan lamari ni ne na cikin gidan Sin, wanda ba wata kasa dake da hurumin tsoma baki a cikinsa.

Dangane da batun tekun kudancin Sin kuwa, kakakin ya ce ba a taba samun wata matsala game da zirga-zirgar jiragen ruwa a sassan tekun ba, kuma har kullum kasar Sin na tsayawa tsayin daka tare da sauran kasashe wadanda batun ya shafa, wajen warware sabani yadda ya kamata, ta hanyar tattaunawa da gudanar da shawarwari, yayin da a hannu guda take kare ikon mulkin kai, da hakkoki da moriyarta daidai da dokoki da ka’idoji masu nasaba. (Saminu Alhassan)

LABARAI MASU NASABA

Babban Jirgin Ruwan Yaki Samfurin 076 Na Sin Ya Kammala Gwajinsa Na Farko A Teku

Sin Ta Gargadi Philippines A Kan Ci Gaba Da Tayar Da Zaune Tsaye A Tekun Kudancinta

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Babban Jirgin Ruwan Yaki Samfurin 076 Na Sin Ya Kammala Gwajinsa Na Farko A Teku
Daga Birnin Sin

Babban Jirgin Ruwan Yaki Samfurin 076 Na Sin Ya Kammala Gwajinsa Na Farko A Teku

November 16, 2025
Sin Ta Gargadi Philippines A Kan Ci Gaba Da Tayar Da Zaune Tsaye A Tekun Kudancinta
Daga Birnin Sin

Sin Ta Gargadi Philippines A Kan Ci Gaba Da Tayar Da Zaune Tsaye A Tekun Kudancinta

November 16, 2025
An Yi Taron Karatun Sinanci Na Duniya Na 2025 A Beijing
Daga Birnin Sin

An Yi Taron Karatun Sinanci Na Duniya Na 2025 A Beijing

November 16, 2025
Next Post
Ranar Yara Ta Duniya: Yadda Shugaba Xi Ya Kasance Tare Da Yara

Ranar Yara Ta Duniya: Yadda Shugaba Xi Ya Kasance Tare Da Yara

LABARAI MASU NASABA

Ƴan Bindiga Sun Sace Mutane 14 A Wani Sabon Hari A Zamfara

Ƴan Bindiga Sun Sace Mutane 14 A Wani Sabon Hari A Zamfara

November 16, 2025
Babban Jirgin Ruwan Yaki Samfurin 076 Na Sin Ya Kammala Gwajinsa Na Farko A Teku

Babban Jirgin Ruwan Yaki Samfurin 076 Na Sin Ya Kammala Gwajinsa Na Farko A Teku

November 16, 2025
Sin Ta Gargadi Philippines A Kan Ci Gaba Da Tayar Da Zaune Tsaye A Tekun Kudancinta

Sin Ta Gargadi Philippines A Kan Ci Gaba Da Tayar Da Zaune Tsaye A Tekun Kudancinta

November 16, 2025
An Yi Taron Karatun Sinanci Na Duniya Na 2025 A Beijing

An Yi Taron Karatun Sinanci Na Duniya Na 2025 A Beijing

November 16, 2025
Ana Mai Da Hankali Kan Dabarun Kasar Sin A Fannin Tinkarar Sauyin Yanayin Duniya A Taron COP30

Ana Mai Da Hankali Kan Dabarun Kasar Sin A Fannin Tinkarar Sauyin Yanayin Duniya A Taron COP30

November 16, 2025
Wata Ƙungiya Ta Fara Bin Digdigin Takardun Karatun Matawalle

Wata Ƙungiya Ta Fara Bin Digdigin Takardun Karatun Matawalle

November 16, 2025
DSS

Hukumar DSS Ta Kama Wani Kan Zargin Ƙerawa Da Rarraba Makamai A Filato

November 16, 2025
ECOWAS

A Zamanantar Da Tsarin Karatu A Makarantun Koyar Da Ilimin Addinin Musulunci – ECOWAS

November 16, 2025
APOSUN Ta Jaddada Aniyarta Na Daƙile Hada-hadar Haramtattun Kuɗaɗe

APOSUN Ta Jaddada Aniyarta Na Daƙile Hada-hadar Haramtattun Kuɗaɗe

November 16, 2025
Yadda Za A Magance Yawan Faɗace-faɗace A Wasannin Gasar Firimiyar Nijeriya

Yadda Za A Magance Yawan Faɗace-faɗace A Wasannin Gasar Firimiyar Nijeriya

November 16, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.