Yara su ne goben duk wata kasa kuma burin ci gaban al’ummar Sinawa. Ci gaba da walwalar yara na cikin muhimman abubuwa da shugaba Xi Jinping ya kudurce a zuciya. Yayin da yake mika sakon gaisuwa ga yaran daukacin sassan kasar Sin yau Lahadi 1 ga watan Yuni, wato ranar yara ta kasa da kasa, wadda kasar ke bikinta tun daga shekarar 2013, shugaba Xi ya kira kansa aboki ga matasa.
Duk da tarin ayyuka dake gabansa, sai da shugaban na Sin ya ware lokaci na zantawa da yara, da ziyartar makarantu, da shiga wasu ayyuka masu nasaba da yara, da amsa wasikun da yaran kasarsa suka aike masa.
Shugaba Xi, ya bayyana muhimmancin tarbiyar yara kanana, da gina basirarsu, da karfin jikinsu, da kuzarinsu na himma da aiki tukuru, inda ya yi kira ga yaran kasar Sin a wannan sabon zamani, da su kasance masu buri da fatan cimma nasarar mafarkansu, kana su nishadantu da karatu da ayyuka, su zamo masu godiya da martaba abota, da kaimin kirkire-kirkire da yunkurin cimma nasara. (Saminu Alhassan)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp