Wani bidiyo da ke yawo a kafafen sada zumunta ya nuna fitaccen malamin addinin Musulunci na Jihar Sakkwato, Sheikh Muhammad Bello Aliyu Yabo, riƙe da bindiga yayin da yake wa’azi, abin da ya jawo cece-kuce a tsakanin jama’a.
A cikin bidiyon na kusan minti biyu, Sheikh Yabo wandawa’azinsa ke da zafi da sukar gwamnati, ya ce duk wanda ya yi yunƙurin kai masa hari zai fuskanci hukunci.
- FRSC Ta Fara Binciken Hatsarin Motar Da Ya Yi Ajalin ’Yan Wasan Kano 22
- Jiragen Yakin NAF Sun Kashe ‘Yan Ta’adda 20, ‘Yan Banga 2 A Zamfara
Yayin da yake magana cikin Harshen Hausa, ya ce, “Ba na jin tsoron mutuwa ko da a daren nan ne. Amma duk wanda ya zo neman raina, ya tabbata ya shirya. Ga abun a hannuna.”
Yana ci gaba da riƙe bindigar, ya ƙara da cewa, “Muddin ina da wannan, ban ga wanda ke da wuƙa da zai iya taɓa ni ba ko da yana cikin maye ne. Amma idan ya gwada, to ni ma na shirya.”
Jaridar LEADERSHIP ta ruwaito cewa ‘yan bindiga sun daɗe suna addabar wasu yankunan Jihar Sakkwato da sauran yankunan Arewa Maso Yamma.
Bidiyon ya jawo martani daban-daban a tsakanin jama’a.
Wasu sun goyi bayan matakin malamin, inda suka bayyana cewa yana da ‘yancin kare kansa a irin wannan lokaci na rashin tsaro.
Amma wasu sun soki abin da ya yi, inda suka ce zuwa da makami wajen taron jama’a ko addini hatsari ne mai girman gaske.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp