Mutum bakwai sun rasa rayukansu sakamakon kifewar wani kwale-kwale a ƙaramar hukumar Shagari da ke Jihar Sakkwato.
Lamarin ya faru ne da safiyar ranar Litinin, a lokacin da fasinjojin ke tafiya daga Gidan Hussaini zuwa ƙauyen Gwargawu, da misalin ƙarfe 9:30 na safe.
- Sabon Shugaban Koriya Ta Kudu Ya Yi Alkawarin Sulhu Da Takwaransa Na Arewa
- Zulum Ya Yaba Wa Sojoji Kan Kashe Babban Kwamandan ISWAP Abu Fatima
Hukumar bayar da agajin gaggawa ta ƙasa (NEMA), ce ta bayyana hakan.
Rahoton NEMA ya ce iska mai ƙarfi ce ta haddasa kifewar jirgin.
Wannan ba shi ne karon farko da irin wannan hatsari ya faru ba.
A watan Oktoban 2024, wani jirgin ruwa ya kife da kusan mutum 300 a Mokwa, na Jihar Neja.
Haka kuma, a watan Satumban 2023, mutum 24 sun mutu a wani hatsarin kwale-kwale a Jihar Neja.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp