Gidauniyar tsohon shugaban majalisar dattawa, Dr Abubakar Bukola Saraki, ta ziyarci garin Mokwa da ke jihar Niger domin jajantawa mutanen garin sakamakon mummunar ambaliyar ruwan da ta afkawa garin wadda ta yi sanadiyar mutuwar daruruwan mutane tare da raba sama da mutum dubu uku da muhallansu.
Wakilan gidauniyar sun fara ziyartar Unguwar Hausawa, inda ambaliyar ta fi yin ɓarna. Kusan gaba ɗaya gidajen garin sun rushe, inda mutane suke zaune babu inda za su zauna. Wakilan gidauniyar sun kuma tattauna da mutanen da abin ya shafa inda suka ji irin halin da suke ciki.
- Fita Daga PDP: Babu Wani Abu Da Zai Cutar Da PDP, Jam’iyyarmu Za Ta Ƙara Haɓaka – Bukola Saraki
- Idan Kana Son Barin PDP, Yanzu Ne Lokacin – Bukola Saraki
Daganan gidauniyar ta sake kai ziyara sansanin da aka ajiye mutanen da suka rasa muhallansu kuma suka tattauna da jami’an Jama’atu Nasril Islam waɗanda suke taimakon da ake kaiwa mutane. An kuma tattauna a kan yadda za a taimakawa mutanen da abin ya shafa.
Wakilan gidauniyar sun sake kai ziyara babban asibitin Mokwa inda suka ziyarci waɗanda suka tsira daga ambaliyar ciki har da ƙananan yara da mata masu ciki waɗanda suke karɓar magani a asibitin. Ma’aikatan asibitin sun ji daɗin ziyarar da gidauniyar ta kai.
Ruƙayya Audu, wata mace ce mai ciki kuma ta tsallake rijiya da baya, a tattaunawar da ta yi da wakilan gidauniyar ta bayyana yadda ta rasa ƴaƴanta guda biyu sakamakon ambaliyar.
Gidauniyar ta kuma kai ziyara fadar Hakimin Mokwa, Alhaji Muhammed Aliyu Shaaba, inda wakilan fadar suka yi maraba da tawagar wakilan gidauniyar tare da jinjina taimako da goyon bayan da aka nuna musu a wannan hali da suke ciki na ibtila’i.
Kamar yadda Babban daraktan yankin, Musa Aliyu ya bayyana, gidauniyar Dr. Abubakar Bukola Saraki ta kai taimakon kuɗi domin tallafawa waɗanda suka tsira da masu taimaka musu. Sannan ya yi kira ga ƙungiyoyi masu zaman kansu da ɗaiɗaikun mutane da su taimakawa al’ummar garin Mokwa.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp