ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Sunday, December 21, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Tattaunawar Da Shugabannin Sin Da Amurka Suka Yi Ta Wayar Tarho Ta Ba Da Jagoranci Ga Dangantakar Dake Tsakanin Kasashen Biyu

by CGTN Hausa and Sulaiman
7 months ago
Amurka

Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya tattauna ta wayar tarho da takwaransa na kasar Amurka Donald Trump, bisa bukatar shugaba Trump. Tattaunawar da aka yi a daren ranar 5 ga wata, ita ce karo na farko tsakanin shugabannin kasashen biyu bayan tsawon watanni sama da hudu.

Idan ana son fahimtar muhimmancin wannan tattaunawa da ma sakon da ya kunsa, wajibi ne a fara fahimtar yanayin da dangantakar Sin da Amurka ke ciki a halin yanzu.

  • Manchester City Ta Kammala Daukar Tijjani Reijnders Daga AC Milan
  • Dalibai Sama Da Miliyan 13 Ne Za Su Rubuta Jarrabawar Shiga Jami’a Ta Kasar Sin

Shawarwarin tattalin arziki da cinikayya da aka gudanar tsakanin kasashen Sin da Amurka a watan da ya wuce a Geneva, ya samu sakamako mai kyau, kuma ya samu karbuwa daga dukkan bangarori. Amma, akwai bambanci sosai game da yadda kasashen Sin da Amurka suka aiwatar da sakamakon da aka cimma wajen shawarwarin. Don sauke nauyin dake wuyanta, Sin ta soke ko dakatar da matakan da suka shafi haraji da ba na haraji ba, wadanda ta dauka domin tinkarar “harajin fito na ramuwar gayya” da Amurka ta sanya. Amma a nata bangaren, Amurka na ci gaba da bullo da manufofin nuna wariya kan kasar Sin, ciki har da takaita fitar da sassan na’urorin laturoni na Chips na AI zuwa ketare, da sanar da soke bizar daliban kasar Sin dake karatu a kasar. Irin wadannan matakai da ta dauka a jere sun saba wa ra’ayin bai daya da aka cimma yayin shawarwarin tattalin arziki da cinikayya na Geneva, tare kuma da lahanta hakki da muradun kasar Sin, haka kuma sun kawo cikas tare da lalata dangantakar dake tsakanin Sin da Amurka.

ADVERTISEMENT

Manazarta suna ganin cewa, a tattaunawar da shugabannin kasashen biyu suka yi a wannan karo, kasar Sin ta bayyana damuwarta da bukatarta a sarari, kuma tana son yin shawarwari da bangaren Amurka don kawar da bambance-bambancen, amma ba za ta taba yarda da matsanancin matsin lambar da Amurka ke yi da ma yadda Amurka ke tattaunawa da ita amma a lokaci guda tana mata zalunci ba, kuma ba za ta sadaukar da matsayinta da yin watsi da ka’idojinta don neman kulla wani abu da ake kira wai yarjejeniya ba.

Ga bangaren Amurka, abun da ya cancanci a daidaita cikin gaggawa shi ne, nuna gaskiya da aiwatar da ra’ayin bai daya da aka cimma yayin shawarwarin Geneva, da soke ayyuka daban-daban na nuna wariya ga kasar Sin, da munanan matakan da ta dauka kan kasar. Kana da yin aiki tare da Sin don ciyar da dangantakar dake tsakanin kasashen biyu gaba, da kawo zaman karko da tabbas ga duniya. (Mai fassara: Bilkisu Xin)

LABARAI MASU NASABA

Yankin Rijiyoyin Mai Na Teku Mafi Girma Na Kasar Sin Ya Ba Da Rahoton Yawan Mai Da Iskar Gas Da Ya Fitar A Shekara

An Bukaci Bunkasa Fannin Kiwo A Hadin Gwiwar Sin Da Afirka

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Yankin Rijiyoyin Mai Na Teku Mafi Girma Na Kasar Sin Ya Ba Da Rahoton Yawan Mai Da Iskar Gas Da Ya Fitar A Shekara
Daga Birnin Sin

Yankin Rijiyoyin Mai Na Teku Mafi Girma Na Kasar Sin Ya Ba Da Rahoton Yawan Mai Da Iskar Gas Da Ya Fitar A Shekara

December 21, 2025
An Bukaci Bunkasa Fannin Kiwo A Hadin Gwiwar Sin Da Afirka
Daga Birnin Sin

An Bukaci Bunkasa Fannin Kiwo A Hadin Gwiwar Sin Da Afirka

December 21, 2025
Wajibi Ne Tawagar MONUSCO Ta Wanzar Da Cin Gashin Kai In Ji Wakilin Kasar Sin
Daga Birnin Sin

Wajibi Ne Tawagar MONUSCO Ta Wanzar Da Cin Gashin Kai In Ji Wakilin Kasar Sin

December 20, 2025
Next Post
An Daure ‘Yan Nijeriya Uku Shekaru 15 A Bisa Laifin Zamba A Indiya

An Daure 'Yan Nijeriya Uku Shekaru 15 A Bisa Laifin Zamba A Indiya

LABARAI MASU NASABA

Davido Zai Raƙashe A Bikin Buɗe Gasar AFCON 2025 A Morocco

Davido Zai Raƙashe A Bikin Buɗe Gasar AFCON 2025 A Morocco

December 21, 2025
Yankin Rijiyoyin Mai Na Teku Mafi Girma Na Kasar Sin Ya Ba Da Rahoton Yawan Mai Da Iskar Gas Da Ya Fitar A Shekara

Yankin Rijiyoyin Mai Na Teku Mafi Girma Na Kasar Sin Ya Ba Da Rahoton Yawan Mai Da Iskar Gas Da Ya Fitar A Shekara

December 21, 2025
An Bukaci Bunkasa Fannin Kiwo A Hadin Gwiwar Sin Da Afirka

An Bukaci Bunkasa Fannin Kiwo A Hadin Gwiwar Sin Da Afirka

December 21, 2025
Akpabio, Ganduje, Ogundoyin Sun Halarci Naɗa Seyi Tinubu Sarauta

Akpabio, Ganduje, Ogundoyin Sun Halarci Naɗa Seyi Tinubu Sarauta

December 21, 2025
Tashar Teku Ta Ciniki Mai ‘Yanci Ta Hainan Ta Bude Sabon Babin Hadin Gwiwar Sin Da Kasashen Afirka

Tashar Teku Ta Ciniki Mai ‘Yanci Ta Hainan Ta Bude Sabon Babin Hadin Gwiwar Sin Da Kasashen Afirka

December 21, 2025
Tinubu

Dambarwar Naɗa Muƙamai Da Soke Su A Gwamnatin Tinubu

December 21, 2025
Zaben Fidda Gwani A APC: Sanatocin Jigawa Sun Rasa Tikitin Komawa Majalisa

APC Za Ta Gudanar Da Babban Taronta Na Kasa A Watan Maris

December 21, 2025
Mun Shirya Tsaf Domin Lashe Gasar AFCON Ta Bana – Bassey

Mun Shirya Tsaf Domin Lashe Gasar AFCON Ta Bana – Bassey

December 21, 2025
Sarakuna Na Da Rawar Takawa Wajen Kare Muhalli A Nijeriya – Ministan Muhalli

Sarakuna Na Da Rawar Takawa Wajen Kare Muhalli A Nijeriya – Ministan Muhalli

December 21, 2025
Me Ya Sa Ake Fifita Ilimin Boko A Kan Na Addini?

Me Ya Sa Ake Fifita Ilimin Boko A Kan Na Addini?

December 21, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.