Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II, ya yi hawa duk da umarnin da rundunar ‘yansandan ta bayar na haramta hawan sallah a jihar.
A maimakon hawan doki kamar yadda aka saba, Sarkin ya yi amfani da motoci a wannan shekarar.
- Sojoji Sun Kashe Babban Kwamandan Boko Haram A Jihar Yobe
- Bam Ya Hallaka Masu Yawon Sallah A Sakkwato
Hawan ya fara ne daga fadar Ƙofar Kudu, inda Sarkin, tare da manyan mutane, hakimai, da magoya baya, suka tafi garin Fanisau, da ke ƙaramar hukumar Ungoggo.
Duk da ba a yi amfani da doki ba, hawan sallar ya kasance cikin murna da farin ciki.
Jama’a sun yi dafifi a kan tituna inda suka yi wa Sarkin rakiya har zuwa garin Fanisau.
Wannan ita ce shekara ta biyu a jere da ‘yansandan Jihar Kano na haramta hawan sallah, wanda suka ce hakan na da nasaba da tsaro.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp