Mukaddashin Kwanturola-Janar na Hukumar Kula da Shige da Fice ta Kasa, (NIS), Idris Jere, ya ce hukumar na shirin daukar karin sabbin ma’aikata 5,000.
Jere, wanda ya bayyana hakan a lokacin da yake amsa tambayoyi daga manema labarai a Dutse a jiya Asabar, ya ce matakin na da nufin magance matsalar karancin ma’aikata a hukumar ta NIS.
- Ga Yadda Kasar Sin Ta Samu Ci Gaba Cikin Shekaru 10 Da Suka Gabata
- Auren Dole: Daya Daga Cikin Fasinjojin Jirgin Kasan Kaduna-Abuja Za Ta Angwance Da Dan Ta’adda
“Game da rashin isassun ma’aikata a NIS, kamar yadda kuka sani, yanzu mun kammala daukar ma’aikata kuma muna horar da wadanda aka dauka a halin yanzu.
“Kamar yadda kuka sani, gwamnati ta sanya takunkumin daukar ma’aikata, amma ta dage hakan a kan hukumomin tsaro, domin tsaro shi ne mafi muhimmanci.
“Don haka, mun rubuta wa shugaban kasa kuma na tabbata za mu samu amincewar daukar karin ma’aikata kusan 5,000 a cikin NIS,” in ji Jere.
Ya kara da cewa ministan harkokin cikin gida, Rauf Aregbesola, ya aike da takardar ga shugaban kasa Muhammadu Buhari, wanda ya nuna aniyarsa ta amincewa da bukatar daukar sabbin ma’aikatan.