Shugaban majalisar sarakunan gargajiya na babban birnin tarayya, Abuja ya amince da hukumar da ke yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi (NDLEA) ta dinga gudanar da gwajin kwayoyi ga masu shirin aure.
BBC Hausa ta rahoto cewa, shugaban majalisa, Sarkin Abaji, Alhaji Adamu Yunusa, shi ne ya bayar da wannan umarni tare da kira a fara aiwatar da wannan tsari nan take.
Wannan tsarin zai tabbatar da cewa dole masu son yin aure su gabatar da shaidar gwajin kwayoyi kafin a daura musu aure.
In ba a manta ba, Tun a watan Oktoba na 2021 ne hukumar NDLEA ta kawo shawarar gudanar da wannan gwaji na tilas.
Shugaban hukumra, Birgediya Janar Buba Marwa mai ritaya ya bayyana cewa tilasta wa masu son yin aure yin wannan gwajin zai rage yadda mutane ke ta’ammuli da kwayoyi a kasar nan.
Sarkin Abaji ya jaddada cewa ta’ammuli da miyagun kwayoyi matsala ce babba ga Nijeriya inda matsalar ta shafi matasa – maza da mata har da ma’aurata.