Alkaluman da aka fitar a hukumance yau Laraba sun nuna cewa, hadin gwiwar tattalin arziki da cinikayya tsakanin Sin da Afirka ya nuna matukar samun habaka bisa karuwar hada-hadar kasuwanci cikin hanzari a shekaru 25 da suka gabata.
A cewar babbar hukumar kwastam ta kasar (GAC), jimillar kudin kayayyakin da kasar Sin ta shigo da su da kuma fitar da su a tsakaninta da Afirka ta karu daga kasa da yuan biliyan 100, watau kimanin dalar Amurka biliyan 13.9 a shekarar 2000 zuwa yuan triliyan 2.1 a shekarar 2024, wanda ya nuna matsakaicin karuwar da aka samu da kashi 14.2 cikin dari a mizanin duk shekara.
An fitar da bayanan ne gabanin bikin baje kolin tattalin arziki da cinikayya tsakanin Sin da Afirka karo na hudu, wanda aka shirya gudanarwa tsakanin ranekun 12 zuwa 15 ga watan Yuni a birnin Changsha, babban birnin lardin Hunan na tsakiyar kasar Sin.
Zuwa karshen shekarar 2024, kasar Sin ta kasance abokiyar cinikayya mafi girma ga kasashen nahiyar Afirka tsawon shekaru 16 a jere, kana ana ci gaba da samun bunkasar cinikayyar bangarorin biyu a shekarar 2025 da muke ciki. (Abdulrazaq Yahuza Jere).
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp