Shugaba Bola Tinubu ya bayyana cewa, Nijeriya ba za ta taba zama kasa mai jam’iyya daya ba a karkashin shugabancinsa, yana mai jaddada kudirinsa na tabbatar da ‘yancin jam’iyyu don ci gaban dimokuradiyya da tsarin mulki.
A yayin da yake gabatar da jawabi a taron hadin guiwar Majalisar Dokokin kasar na bikin cika shekaru 26 na zagayowar ranar Dimokuradiyya, Shugaba Tinubu ya yi raddi ga masu sukar jam’iyyar APC mai mulki da cewa, tana kokarin kawar da jam’iyyun adawa.
- An Bude Baje Kolin Tattalin Arziki Da Cinikayya Na Sin Da Afirka A Changsha
- Aliko Dangote Ya Sauka Daga Shugabancin Kamfanin Sukarin Dangote
“Ga wadanda suka yi korafin cewa, jam’iyyar APC na da niyyar kafa jam’iyya daya, na yi muku alkawari, hakan ba za ta faru ba”.
Da yake tuna tarihin siyasarsa a matsayin daya daga cikin gwamnonin adawa a farkon shekarun 2000, Tinubu ya sake jaddada matsayinsa a matsayin mai kare dimokradiyyar jam’iyyun adawa.
Ya kuma mika godiyarsa ga magabacinsa, tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari, bisa yadda ya fahimci tare da gyara abin da ya bayyana a matsayin “kuskuren zaben 1993,” wanda aka yi imani da cewa, Cif Moshood Abiola da Alhaji Babagana Kingibe ne suka lashe amma gwamnatin soja ta soke zaben.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp