• English
  • Business News
Tuesday, October 21, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Kula Da Kanki Bayan Haihuwa Abu Ne Muhimmi

by Bilkisu Tijjani and Sulaiman
4 months ago
Haihuwa

Babban hatsarin da haihuwa ke zuwa da shi dake jawo asarar rayukan mata bayan haihuwa shi ne zubar jini bayan haihuwar wato Post Partum Hemorrhage a likitance dake faruwa. Wannan shi ne lokacin da dariya ke rikidewa ta koma kuka, wato murna ta koma ciki, daga murnar haihuwa a koma kukan mutuwa.

Sau tari wanda bai sani ba zai tunanin fitar yaro shi ne haihuwa lafiya, shi ne mafi mahimmanci. Amma wannan ba shi ne haihuwa lafiya ba. Haihuwa lafiya shi ne a ga bayan fitar yaro Mahaifa ta murda ta harba wato contracton ta yadda hakan zai sanadiyar fitowar placenta wato (mabiyiya ko abin da Hausa kance uwa ta biya). Kai wani lokacin koda uwa ta biya akwai bukatar sai mahaifa ta yi wannan harbawar. Idan ba ta harba ba hakan ba zai sa jijiyoyin jini su toshe ba don haka mace za ta ci gaba da zubar da jini, wanda wannan shike kashe mace. Wani lokacin hatsarin placenta din ce ma ke manne mahaifar ta yadda in aka jawo sai de ta taho hade da mahaifar ta tidota. Shi ya sa haihuwa tsallake siradi ce ba karami ba.

  • Gwamnatin Tarayya Ta Ƙaddamar Da Addu’ar Kwana 3 Don Samun Isasshen Abinci
  • Kudaden Da Ake Karba A Kogin Hadejia Jama’are Daga Hannun Manoma, Ba Haraji Ba Ne – HJRBDA

Toh abin da ke taimaka wa wannan harbawar shi ne ai maza-maza ai stimulating maman mace, shi ya sa wani lokacin ma in mace na nakuda akan iya bukatar a kawo yaron da take shayarwa domin ya kama maman hakan zai taimaka wajen contraction din mahaifarta, ko kuma in ba yaro a ce mijinta ya tsaya ya rika kama mamanta, in babu duk daya sai dai nurses su yi mata.

To waccan hikimar ta stimulating nipple na da matukar mahimmanci har bayan haihuwa, wannan ta sanya game kallon fina-finan likitoci na haihuwa za ku ga da an ciro yaro cikin jininsa da komai za’a dora wa uwa shi ya kama mama domin ya taimakamata ya sa mahaifarta harbawa jinin haihuwa ya tsaya, wannan ita ce hikimar fata zuwa fata, nan da nan za ku ga likitoci sun dorasa a mama saboda hatsarin daka iya biyo baya.

Haka zalika wannan jinin haihuwar duk da an fi ganin zubarsa nan da nan bayan haihuwa cikin awa 24 na yini. Haka zalika kananan ma’aikatan lafiya ku sani yana iya faruwa tun daga bayan kwana 1 da haihuwa zuwa sati 6. Matuwar macen da aka san ta haihu kasa da sati 6 ta zo asibiti da complaint na zubar jini to ku sani yana iya kasancewa Post Partum Hemorrhage har sai in kun gano wani abun daban, don haka a lura da kyau, kar a dau zubar jini matsayin ba mai tsanani ba abu ba don kurum kila an yi satuttuka da haihuwa ko kwana 3 uku.

LABARAI MASU NASABA

Kar Ki Yi Kuskuren Da Za Ki Yi Da Na Sani A Kai (2)

Kar Ki Yi Kuskuren Da Za Ki Yi Da Na Sani A Kai (1)

Haka zalika koda ba ki fuskanci matsalar zubar jini ba, ki daure ki shayar da jaririnki hakan zai ci gaba da sa mahaifarki harbawa ta taso daga mararki ta koma kasan cikinki cikin sati 2 da haihuwa, hakan zai rage miki tsananin ciwon mara duk da shayarwa akwai zafi wani lokacin.

Za Mu Ci Gaba Mako Mai Zuwa Insha Allahu

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Kar Ki Yi Kuskuren Da Za Ki Yi Da Na Sani A Kai (1)
Uwargida Sarautar Mata

Kar Ki Yi Kuskuren Da Za Ki Yi Da Na Sani A Kai (2)

October 19, 2025
Kar Ki Yi Kuskuren Da Za Ki Yi Da Na Sani A Kai (1)
Uwargida Sarautar Mata

Kar Ki Yi Kuskuren Da Za Ki Yi Da Na Sani A Kai (1)

October 12, 2025
Gwamnonin Arewa Sun Amince Da Kafa Ƴansandan Jihohi: Ko Hakan Zai Yi Tasiri Ga Sha’anin Tsaro?
Uwargida Sarautar Mata

Gwamnonin Arewa Sun Amince Da Kafa Ƴansandan Jihohi: Ko Hakan Zai Yi Tasiri Ga Sha’anin Tsaro?

September 12, 2025
Next Post
Yadda Cinikin Bayi Ya Fara A Nahiyar Afirka (1)

Yadda Cinikin Bayi Ya Fara A Nahiyar Afirka (1)

LABARAI MASU NASABA

An Ɗage Shari’ar Shugabannin Ƙungiyar Ansaru Zuwa 19 Ga Watan Nuwamba

An Ɗage Shari’ar Shugabannin Ƙungiyar Ansaru Zuwa 19 Ga Watan Nuwamba

October 21, 2025
Shirin Raya Kasa Na Shekaru Biyar Biyar: Sirrin Kasar Sin Na Saurin Bunkasa

Shirin Raya Kasa Na Shekaru Biyar Biyar: Sirrin Kasar Sin Na Saurin Bunkasa

October 21, 2025
Mutane 3,433 Sun Rasu a Hatsarin Mota 6,858 Cikin Wata 9 A Nijeriya – FRSC

Mutane 3,433 Sun Rasu a Hatsarin Mota 6,858 Cikin Wata 9 A Nijeriya – FRSC

October 21, 2025
NLC Ta Bai Wa Gwamnatin Tarayya Wa’adin Mako 4 Don Biyan Buƙatun ASUU Da Sauran Ƙungiyoyi 

NLC Ta Bai Wa Gwamnatin Tarayya Wa’adin Mako 4 Don Biyan Buƙatun ASUU Da Sauran Ƙungiyoyi 

October 21, 2025
‘Yansanda Sun Kama Ɗan Bindiga Da Kuɗin Fansa Naira Miliyan 5 A Delta

’Yansanda Sun Kama Ɗan Fashi Sanye Da Kayan NYSC A Enugu

October 21, 2025
Gwamnatin Gombe Ta Ceto Yara 59 Da Aka Yi Safararsu

Gwamnatin Gombe Ta Ceto Yara 59 Da Aka Yi Safararsu

October 21, 2025
Matsayar Kasar Sin A Bayyane Take Dangane Da Batutuwan Cinikayya Da Tsagin Amurka

Matsayar Kasar Sin A Bayyane Take Dangane Da Batutuwan Cinikayya Da Tsagin Amurka

October 20, 2025
An Shiga Ruɗani A Borno Bayan Budurwa Ta Kashe Kanta Saboda Auren Dole

An Shiga Ruɗani A Borno Bayan Budurwa Ta Kashe Kanta Saboda Auren Dole

October 20, 2025
Sin Ta Kara Wasu Wurare 22 Cikin Yankunan Dausayi Masu Matukar Muhimmanci A Kasar

Sin Ta Kara Wasu Wurare 22 Cikin Yankunan Dausayi Masu Matukar Muhimmanci A Kasar

October 20, 2025
Tinubu Ya Taya Kwankwaso Murnar Ranar Haihuwa, Ya Jaddada Abotarsu

Tinubu Ya Taya Kwankwaso Murnar Ranar Haihuwa, Ya Jaddada Abotarsu

October 20, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.