• English
  • Business News
Monday, November 10, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Hadin Gwiwar Sin Da Afirka Na Kara Habaka Daga Manyan Tsare-Tsare Zuwa Matakai Na Ainihi

by Sulaiman
5 months ago
Sin

LABARAI MASU NASABA

Bikin Baje Kolin CIIE: Da Abokin Daka Ake Shan Gari

Bikin Baje Kolin CIIE Zai Samarwa Najeriya Karin Damammaki

An rufe taron ministocin Sin da Afirka mai tabbatar da ci gaban hadin gwiwar da aka samu a dandalin tattaunawar hadin kan Sin da Afirka wato FOCAC, wanda aka gudanar daga ranekun 10 zuwa 12 a birnin Changsha na lardin Hunan, matakin da ya bayar da sabbin damammaki ga kasashen Afirka, bisa shirin “manyan ayyuka 10 na abota tsakanin Sin da Afirka”. Sa’an nan, bayan an kammala taron, nan take, an kaddamar da bikin baje kolin kayayyaki hajojin Sin da Afirka karo na 4, duk a birnin Changsha, matakin da ya zamo daya daga cikin jerin ayyukan da ake gudanar da su don aiwatar da shirin “manyan ayyuka 10”, inda aka baje kolin ci gaban da aka samu, da tattara damammaki da albarkatu wuri guda, domin gaggauta samun ingantacciyar bunkasar hadin gwiwar Sin da Afrika a bangaren ciniki da tattalin arziki.

A cikin shekaru 25 da suka gabata, tun kafuwar FOCAC a shekarar 2000, yawan kudin kayayyakin da ake shigarwa da na fitarwa tsakanin Sin da Afirka ya karu zuwa dalar Amurka biliyan 292.4 a shekarar 2024 daga dalar biliyan 13.9 a 2000, inda adadin ya karu da fiye da ninki 20. Kana a cikin wasikar da shugaban kasar Sin Xi Jinping ya aika don taya murnar cimma nasarar gudanar da taron ministoci na wannan karo, Xi ya sanar da shirin yafe harajin kwastam na kaso 100% a kan kayayyakin kasashen Afirka 53, wadanda suka kulla dangantakar diflomasiyya da Sin, matakin da zai kara saukaka wa kasashen Afirka a fannin fitar da kayayyakinsu zuwa kasar Sin.

Kazalika, a farkon watanni 5 na bana, yawan kudin da Sin ta kashe wajen shigo da kayayyakin Afrika zuwa cikin kasarta ya kai dalar Amurka biliyan 50.6, adadin da ya karu da kashi 1.6% bisa na makamancin lokacin bara. Hakan ya ba kasashen Afirka damar more babbar kasuwar Sin.

Hadin gwiwar Sin da Afirka na kara habaka, duba da yadda ake aiwatar da hakikanan matakai don tabbatar da manyan tsare-tsare da aka cimma, tare da mai da hankali matuka kan amfanar da al’ummun Afirka, da inganta karfin kasashen Afirka na samun bunkasuwa bisa dogaro da kai. Ma iya cewa, hadin gwiwar bangarorin Afirka da Sin ta fuskar ciniki da tattalin arizki na cikin wani yanayi mai armashi da dorewa, duk da kalubaloli, da sauye-sauyen yanayin da ake fuskanta a duniya, abin da sa ake samun cikakken kwarin gwiwa bisa hadin gwiwar kasashe masu tasowa da bunkasar duniya baki daya. (Mai zane da rubutu:MINA)

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Bikin Baje Kolin CIIE: Da Abokin Daka Ake Shan Gari
Ra'ayi Riga

Bikin Baje Kolin CIIE: Da Abokin Daka Ake Shan Gari

November 6, 2025
Bikin Baje Kolin CIIE Zai Samarwa Najeriya Karin Damammaki
Ra'ayi Riga

Bikin Baje Kolin CIIE Zai Samarwa Najeriya Karin Damammaki

November 4, 2025
Sin Ta Yi Allah Wadai Da Illata Fararen Hula Tare Da Fatan Gaggauta Kawo Karshen Yaki A Sudan
Ra'ayi Riga

Sin Ta Yi Allah Wadai Da Illata Fararen Hula Tare Da Fatan Gaggauta Kawo Karshen Yaki A Sudan

November 4, 2025
Next Post
Sin Ta Yi Kira Ga Isra’ila Da Ta Dakatar Da Kaddamar Da Hare-hare Kan Iran

Sin Ta Yi Kira Ga Isra’ila Da Ta Dakatar Da Kaddamar Da Hare-hare Kan Iran

LABARAI MASU NASABA

Da Dumi-duminsa: ‘Yan Bindiga Sun Yi Garkuwa Da Basarake A Ondo

Wani Sabon Hari Kan Al’ummar Da Ke Iyaka Da Katsina A Kano Ya Rutsa Da Mata 5

November 10, 2025
Matatun mai

Yadda Sojoji Suka Tarwatsa Haramtattun Matatun Mai 14 A Yankin Neja Delta 

November 10, 2025
Jibrin Kofa

Ɗan Majalisar Wakilai, Jibrin Ƙofa Ya Sauya Sheƙa Daga NNPP Zuwa APC

November 10, 2025
Boko haram

Sojoji Sun Fatattaki Boko Haram, Sun Ceto Mutane 86 Da Aka Sace A Borno

November 10, 2025
Hadin Gwiwar Sin Da Afirka Na Ci Gaba Da Zama Muhimmin Ginshiki Ga Ci Gaban Nahiyar 

Hadin Gwiwar Sin Da Afirka Na Ci Gaba Da Zama Muhimmin Ginshiki Ga Ci Gaban Nahiyar 

November 9, 2025
An Rufe Taron Kolin Wuzhen Na Ayyukan Yanar Gizo Na Duniya Na Shekarar 2025

An Rufe Taron Kolin Wuzhen Na Ayyukan Yanar Gizo Na Duniya Na Shekarar 2025

November 9, 2025
Katsina United Ta Shiga Komar Hukuncin Hukumar NPFL

Katsina United Ta Shiga Komar Hukuncin Hukumar NPFL

November 9, 2025
Xi Ya Gana Da Shugabar IOC Tare Da Shugaban IOC Na Karramawa

Xi Ya Gana Da Shugabar IOC Tare Da Shugaban IOC Na Karramawa

November 9, 2025
CMG Ya Cimma Yarjejeniyar Samun Iznin Watsa Shirye-shiryen Wasannin Olympics Daga Shekarar 2026 Zuwa 2032

CMG Ya Cimma Yarjejeniyar Samun Iznin Watsa Shirye-shiryen Wasannin Olympics Daga Shekarar 2026 Zuwa 2032

November 9, 2025
Kasar Sin Ta Yi Nasarar Harba Sabbin Taurarin Dan Adam Na Gwaji

Kasar Sin Ta Yi Nasarar Harba Sabbin Taurarin Dan Adam Na Gwaji

November 9, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.