Shugaba Bola Tinubu ya sauya shirinsa na kai ziyara Jihar Kaduna a ranar Laraba, 18 ga watan Yuni, 2025, inda zai tafi Jihar Benuwe domin magance rikice-rikicen da ke faruwa a jihar.
Mai magana da yawun shugaban ƙasa, Bayo Onanuga, ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar da yammacin ranar Litinin.
- Hauhawar Farashi Ya Sauka Zuwa Kashi 22.9 A Watan Mayun 2025
- An Daddale Tarin Yarjejeniyoyi Yayin Taron Baje Kolin Harkokin Tattalin Arziki Da Cinikayya Na Sin Da Afirka
A cewar sanarwar, Shugaba Tinubu na son ganin halin da ake ciki da kansa da kuma ganawa da manyan mutane a jihar, ciki har da sarakunan gargajiya, shugabannin siyasa da addini, shugabannin al’umma da ƙungiyoyin matasa.
Manufarsa ita ce samo mafita mai ɗorewa ga rikicin da ya jawo asarar rayuka mai yawa.
Kafin zuwansa, Shugaba Tinubu ya riga ya aike da manyan jami’an gwamnati da tsaro zuwa Benuwe, ciki har da Sakataren Gwamnatin Tarayya, Sufeto-Janar Janar na Ƴansanda, da shugabannin hukumomin leƙen asiri da kwamitocin tsaro na majalisar dokoki.
Za a gudanar da taron jin ra’ayin jama’a a lokacin ziyarar shugaban ƙasa.
Tun da farko, Tinubu ya yi Allah-wadai da rikicin da ke faruwa a Benuwe, inda ya yi kira da a zauna lafiya.
Haka kuma, ya miƙa ta’aziyyarsa ga iyalan waɗanda suka rasa rayukansu da dukiyoyinsu a sanadin rikicin.
Tinubu ya shirya kai ziyara Jihar Kaduna a ranar Laraba domin ƙaddamar da ayyukan gwamnatin jihar, amma yanzu ya ɗage ziyarar zuwa ranar Alhamis, 19 ga watan Yuni, 2025.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp