• English
  • Business News
Monday, November 3, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Daga Taklimakan Zuwa Sahara: Karin Abubuwan Al’ajabi Na Faruwa Bisa Hadin Gwiwar Sin Da Afirka A Fannin Yaki Da Kwararar Hamada

by CGTN Hausa and Sulaiman
5 months ago
Sahara

Jama’a, ko kun taba ganin furannin Rose da suka bude a cikin hamada? 

Lallai, wannan abu ne da ya faru a hakika a hamadar Taklimakan da ke kasar Sin. A kwanan nan, furannin Rose kimanin dubu 100 ne suka bude a iyakar hamadar, lamarin da ya shaida karin nasara da kasar Sin ta samu ta fannin yaki da kwararar hamada.

Taklimakan tana jihar Xinjiang da ke arewa maso yammacin kasar Sin, hamada ce mafi girma ta kasar Sin, wadda kuma ta kasance muhimmin fagen yaki da kwararar hamada a kasar Sin. A sassan kudancin hamadar da aka fi samun iska mai karfi, tuddan rairayi su kan mamaye dausayi da kimanin mita 2 zuwa 5 a kowace shekara, kuma yadda za a tsayar da hamadar babban aiki ne da jihar ta Xinjiang ke sanyawa gaba wajen kiyaye muhalli. Bisa kokarin da masanan yaki da kwararar hamada da ma mazauna wurin suka shafe gomman shekaru suna yi, daga karshe suka cimma nasarar kewaye hamadar da wani shingen itatuwa mai tsawon kilomita 3046 a ranar 28 ga watan Nuwamban bara, shingen da ya kasance irinsa mafi tsawo da aka kafa a duniya. Furannin Rose da suka bude kwanan nan kuma, sun kasance sashe na karshe da aka dasa a wannan babban aiki. Bisa nazarin da masu binciken kimiyya na wurin suka yi a kan hamada da bugowar iska da ma yanayin ruwa na wurin, sun gano dabarar dasa furannin Rose da suka iya jure yanayin hamadar, har ma ga shi a yau, furannin sun zamanto wani shinge mai karfi da ke iya kare iska da ma rairayi.

A hakika, shingen itatuwa da aka yi amfani da shi wajen kewaya hamadar Taklimakan wani misali ne da ya shaida gaggaruman nasarorin da kasar Sin ta samu ta fannin yaki da kwararar hamada. Daga hamadar Maowusu zuwa Kubuqi, cikin gomman shekaru da suka wuce, kasar Sin ta samu nasarorin a-zo-a-gani ta fannin yaki da kwararar hamada, har ma ta samu babban yabo daga gamayyar kasa da kasa.

Ba a kasar Sin kadai ba ce, kwararar hamada kalubale ne ga kasashen duniya baki daya. A nahiyar Afirka, matsalar ta dade tana addabar kasashen yankin Sahel. A kasar Mauritania, kusan kashi 2/3 na fadin kasar na cikin hamadar Sahara, kuma matsalolin fari na kwararar hamada suna haifar da munanan illoli ga ci gaban kasar. Sai dai yanayin ya fara sauyawa. A kauyen Bir El Barka na yankin Trarza da ke yammacin kasar, an shimfida bututun ban ruwa nau’in ‘drip irrigation’ a Turance, ga shi kuma tsiron ganyayen lambu sun fito daga gonar rairayi. A gefen gonar kuma, allunan samar da wutar lantarki ta hasken rana suna samar da lantarki ga famfuna don fitar da ruwa daga karkashin kasa zuwa gonaki. Lallai wannan lambun nune-nunen fasahohin yaki da kwararar hamada na tsakanin Sin da kasashen Afirka reshen kasar Mauritania ya kayatar sosai. A can wajen, bisa gudummawar da masanan kasar Sin suka bayar, an mai da hamadar ta zama dausayi bisa ingantattun fasahohi na kasar Sin, har ma an kai ga yin gwajin shuka nau’o’in amfanin gona tare da samun girbin wasunsu.

LABARAI MASU NASABA

A Kan Wa Trump Ke Son Kaddamar Da Hari a Najeriya?

Duk Da Barazanar Tattalin Arzikin Duniya, Kasar Sin Ta Sanya Tabbaci Da Kwanciyar Hankali A Duniyarmu Mai Cike Da Ruɗani

Sinawa tun zamanin baya na ganin cewa, samun dadi ga kowa shi ne dadi na gaske. A zamanin yanzu, kasar Sin ba kawai take jin dadin sauye-sauyen da ke faruwa a sassan hamada na kasar ba, hatta ma tana fatan ganin karin yankunan hamada sun zama dausayi a fadin duniya. Don haka, take kokarin bayar da fasahohinta ga kasashen Afirka da su ma suke fuskantar kalubalen kwararar hamada. Bisa nazarin da masanan Sin da kasashen Afirka suka yi, sun gano cewa, fadin sassan hamada a yankin Sahel ya ragu daga kaso 72,31% zuwa 69.23% tsakanin shekarar 2000 zuwa ta 2020.

Daga Taklimakan zuwa Sahara, karin abubuwan al’ajabi na ci gaba da faruwa bisa hadin gwiwar Sin da kasashen Afirka ta fannin yaki da kwararar hamada.

 

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

A Kan Wa Trump Ke Son Kaddamar Da Hari a Najeriya?
Ra'ayi Riga

A Kan Wa Trump Ke Son Kaddamar Da Hari a Najeriya?

November 2, 2025
Duk Da Barazanar Tattalin Arzikin Duniya, Kasar Sin Ta Sanya Tabbaci Da Kwanciyar Hankali A Duniyarmu Mai Cike Da Ruɗani
Ra'ayi Riga

Duk Da Barazanar Tattalin Arzikin Duniya, Kasar Sin Ta Sanya Tabbaci Da Kwanciyar Hankali A Duniyarmu Mai Cike Da Ruɗani

October 28, 2025
Me Ya Sa Kasar Sin Ke Son Ganin Ci Gaban Kasashen Afirka?
Ra'ayi Riga

Me Ya Sa Kasar Sin Ke Son Ganin Ci Gaban Kasashen Afirka?

October 27, 2025
Next Post
Xi Ya Gabatar Da Muhimmin Jawabi A Taron Koli Na Sin Da Kasashen Tsakiyar Asiya Karo Na Biyu

Xi Ya Gabatar Da Muhimmin Jawabi A Taron Koli Na Sin Da Kasashen Tsakiyar Asiya Karo Na Biyu

LABARAI MASU NASABA

Kwankwaso Ya Gargaɗi Trump Kan Barazana Ga Nijeriya

Kwankwaso Ya Gargaɗi Trump Kan Barazana Ga Nijeriya

November 2, 2025
Gumi Ya Nemi Nijeriya Ta Katse Hulɗa Da Amurka Idan Trump Bai Janye Barazanar Sa Ba

Gumi Ya Nemi Nijeriya Ta Katse Hulɗa Da Amurka Idan Trump Bai Janye Barazanar Sa Ba

November 2, 2025
Shugaba Xi Ya Mika Sakon Taya Murnar Bude Babban Gidan Tarihi Na Kasar Masar

Shugaba Xi Ya Mika Sakon Taya Murnar Bude Babban Gidan Tarihi Na Kasar Masar

November 2, 2025
Ƙasashen Da Ba Su Yanke Hukuncin Kisa A Duniya Ba

Ƙasashen Da Ba Su Yanke Hukuncin Kisa A Duniya Ba

November 2, 2025
Ziyarar Shugaba Xi A Koriya Ta Kudu Ta Bude Babin Yaukaka Hadin Gwiwar Yankin Asiya Da Fasifik

Ziyarar Shugaba Xi A Koriya Ta Kudu Ta Bude Babin Yaukaka Hadin Gwiwar Yankin Asiya Da Fasifik

November 2, 2025
Yadda Za Ku Hada Fab Biskit

Yadda Za Ku Hada Fab Biskit

November 2, 2025
Kano Pillars Ta Koma Matsayi Na 20 Bayan Shan Kashi A Hannun Enyimba

Kano Pillars Ta Koma Matsayi Na 20 Bayan Shan Kashi A Hannun Enyimba

November 2, 2025
Wolves Ta Kori Da Kocinta Vitor Pereira Sakamakon Rashin Nasara

Wolves Ta Kori Da Kocinta Vitor Pereira Sakamakon Rashin Nasara

November 2, 2025
Musabbabin Hana Sule Lamido Fom Ɗin Takarar Shugabancin PDP

2027: Yadda Gwamnoni Suka Yi Fatali Da Mataimakansu Wajen Zaɓo Waɗanda Za Su Gaje Su

November 2, 2025
Gidauniyar IRM Da KADCHMA Ta Ƙaddamar Da Inshorar Lafiya Kyauta Ga Mutane 200 A Kaduna

Gidauniyar IRM Da KADCHMA Ta Ƙaddamar Da Inshorar Lafiya Kyauta Ga Mutane 200 A Kaduna

November 2, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.